Kano: Kotu Ta Takawa APC da PDP Burki kan Zaben Kananan Hukumomi da Za a Yi

Kano: Kotu Ta Takawa APC da PDP Burki kan Zaben Kananan Hukumomi da Za a Yi

  • Wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da jam'iyyun APC da PDP daga kawo cikas ga hukumar zaben jihar Kano (KANSIEC)
  • Kotun ta dakile jam'iyyun siyasa 21 daga hana hukumar karbar kudin fom na takara da ta gindaya tun farko kan zaben na Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan korafin jam'iyyun kan yawan kudin takara da hukumar ta gindaya wanda a cewarsu ya yi yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta yi zama kan korafin jam'iyyun APC da PDP game da zaben kananan hukumomi.

Kotun ta dakatar da APC da PDP da kuma jam'yyu 19 daga hana hukumar zaben jihar (KANSIEC) karbar kudin fom din takara.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar rikici a Edo: 'Yan sanda sun dauki matakai bayan nasarar APC

Kotu ta dakile PDP da APC a zaben kananan hukumomi a Kano
Kotu ya dakatar da PDP da APC shiga hurumin hukumar KANSIEC a Kano. Hoto: All Progressives Congress, Peoples Democratic Party.
Asali: Facebook

Kotu ta dakile PDP, APC a zaben Kano

Leadership ta ruwaito cewa kotun ta yi hukuncin ne bayan zanga-zanga da jam'iyyun siyasa suka yi kan yawan kudin siyan fom na takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, hukumar KANSIEC ta sanya N10m da kuma N5m domin siyan fom na takarar shugaban karamar hukuma da kansila a jere.

Jam'iyyun sun koka kan yadda kudin siyan fom din ya yi yayin da ake shirin yin zaben a ranar 24 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Daily Post.

Kotu ta bukaci KANSIEC ta yi gaban kanta

Kotun ta umarci barin hukumar KANSIEC ta yi gaban kanta wurin karbar kuɗin fom da cigaba da shirin gudanar da zaben da za a yi.

Daga bisani, kotun ta dage cigaba da sauraran shari'ar har zuwa ranar 10 ga watan Oktobar 2024 domin jin korafe-korafe.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Jerin kananan hukumomin da Ighodalo na PDP ya lashe

PDP ta fita a zaben kananan hukumomi

Kun ji cewa bayan shirya zaben kananan hukumomi a watan Oktoban 2024 a Jigawa, jam'iyyar PDP ta janye shiga zaben.

Jam'iyyar ta zargi hukumar zaben jihar ta SIEC da tsauwalawa a kudin siyan fom na takara tare da zargin taya APC yin magudi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar a jihar, Hon. Ali Idris Diginsa ya fitar a ranar Larabar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.