Kano: 'Yan Adawa Sun Saka Abba a Gaba, Fitattun 'Yan Kannywood Sun Koma APC
- Siyasar Kano na cigaba da daukan hankulan al'ummar Arewacin Najeriya yayin da ake cigaba da samun masu sauya sheka a jihar
- A wannan karon, an samu wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka ajiye tafiyar Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi jaruman Kannywood din a birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Siyasar Kano na cigaba da daukan salo yayin da jam'iyyar APC ke cigaba da yi wa NNPP illa.
An samu wasu fitattun jaruman Kannywood da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Legit ta tatttaro bayanai kan sauya sheƙar ne a cikin wani sako da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitattun 'yan Kannywood sun koma APC
Shahararren mawaki a masana'antar fim ta Kannywood, Nura M. Inuwa ya koma jam'iyyar APC karkashin Sanata Barau Jibrin.
Rahotanni sun nuna cewa Nura M. Inuwa ya sauya sheka ne tare da wasu jaruman Kannywood da suka hada da Fati Muhammad da sauransu.
Ko a kwanakin baya wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka hada da Rabi'u Daushe sun fice daga NNPP zuwa APC a jihar Kano.
Barau ya karbi 'yan Kannywood a APC
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ne ya karɓi tawagar yan Kannywood din a Abuja.
Sanata Barau Jibrin ya ce shigowar jaruman zuwa APC alama cewa da ke nuna cewa jam'iyyar ta tsayu wajen kawo cigaba a Najeriya.
Ya kuma tabbatar da cewa za su yi aiki tare domin kawo cigaba da magance matsalolin da suka addabi Najeriya a halin yanzu.
NNPP ta samu karuwa a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu daga jam'iyyun adawa su 30 sun koma NNPP mai mulki a jihar bisa wasu dalilai da su ka bayyana.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe su a gidan gwamnati, inda ya yabe su bisa daukar mataki mai kyawun gaske domin kawo cigaba a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng