Kano: NNPP Ta Samu Karuwa,Yan Jam'iyyun Adawa 30 Sun Rungumi Kwankwasiyya

Kano: NNPP Ta Samu Karuwa,Yan Jam'iyyun Adawa 30 Sun Rungumi Kwankwasiyya

  • Wasu daga jam'iyyun adawa su 30 sun koma NNPP mai mulki a jihar Kano bisa wasu dalilai da su ka bayyana
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe su a gidan gwamnati, inda ya yabe su bisa daukar mataki mai kyawun gaske
  • Wadanda suka koma NNPP sun yi hijira ne daga jam'iyyun NRM da ZLP, inda su ka yaba da yadda ake tafiyar da gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi tubabbun yan siyasa daga jam’iyyun adawa guda biyu, inda su ka yi sauyin sheka zuwa jam’iyyar NNPP.

Wasu daga cikin yan jami’iyyar ZLP da NRM ne su ka yanke shawarar ficewa daga cikin jam’iyyunsu bisa mabambantan dalilai.

Kara karanta wannan

Damagum: Jerin gwamnoni 6 da ke goyon bayan a tsige shugaban PDP na kasa

Gwamna
Gwamna Abba ya karbi yan jam'iyyun NRM, ZLP zuwa NNPC Horo: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakon da daraktan yada labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta wallafa a shafinsa na Facebook, an gano daga cikin wadanda su ka rungumi tafiyar NNPP, tsarin Kwankwasiyya sun nemi manyan kujeru a zaben 2023 da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan NNPP ya yi maraba da yan adawa

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi maraba da wasu daga cikin yan jam’iyyun adawa da su ka rungumi jam’iyyarsa ta NNPP.

A sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya bayyana jin dadin yadda su ka farga wajen sauya jam’iyyar da ta dace da su.

Meyasa 'yan jam’iyyun adawa suka bi NNPP

Jagororin da su ka koma NNPP sun bayyana aikin gwamna Abba Kabir Yusuf na ciyar da jama’ar Kano gaba a matsayin abin da ya ja hankalinsu zuwa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

Malam Shehu Nuhu, daya daga cikin jagororin ya ce sun yaba matuka da manyan ayyukan da gwamnan ke yi, musamman a bangaren lafiya da ilimi.

NNPP na shinshino nasarar zaben 2027

A baya mun wallafa cewa jam'iyyar NNPP ta ce akwai kwararan alamun cewa ita ce za ta yi nasara a babban zaben 2027, domin akwai shirye shirye masu zafi.

A ziyarar da ya kai sakatariyar NNPP ta jihar Osun, dan takarar shugaban kasar jam'iyyar a zaben da ya wuce, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce su na da manufa mai kyau kan talaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.