Jigawa: Rundunar Yan Sanda Ta Fitar da Shiri kan Yan Daba gabanin Zabe

Jigawa: Rundunar Yan Sanda Ta Fitar da Shiri kan Yan Daba gabanin Zabe

  • Yan sanda a Jigawa sun fara shirin tabbatar da an yi zaben kananan hukumomi biyar a jihar cikin kwanciyar hankali
  • Kwamishinan yan sandan Jigawa, A.T Abdullahi ne ya bayyana haka, inda ya ce ba za su amince yan daba su kawo tarnaki ba
  • Kwamishinan ya kara da cewa yanzu haka ana aikin zakulo yan bangar siyasa da ka iya zama barazana a zaben mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Yayin da ake shirin zaben kananan hukumomi biyar na jihar Jigawa, rundunar yan sanda ta fara shirin tabbatar da kawar da barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

A ranar 5 Satumba, 2024 ne za a gudanar da zaben, inda yan sanda su ka gargadi dukkanin masu son tayar da hankulan jama'a a lokacin.

Jigawa
Yan sanda za su magance bangar siyasa kafin zaben Jigawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamishinan yan sandan Jigawa, A.T Abdullahi ya sha alwashin dauke dukkanin gagararrun yan daba da su ka addabi jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin yan sandan Jigawa kan zabe

A ranar Talata ne rundunar yan sandan Jigawa ta bayyana cewa ana shirin gano wuraren da 'yan daba ke ya da zango a jihar gabanin zaben kananan hukumomi.

Kwamishinan ya ce jami'an yan sanda za su dauki kwararan matakai na kawar da dukkanin barazanar da yan daban za su haifar a lokutan zaben.

Za a kama yan daba kafin zaben Jigawa

Rundunar yan sandan Jigawa ta bayyana shirin da ta ke yi na kama duk wanda aka san dan bangar siyasa ne a jihar kafin zaben kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar rikici a Edo: 'Yan sanda sun dauki matakai bayan nasarar APC

Kwamishinan ya ce za a kwashe yan bangar siyasan tare da killace su a ofishin yan sanda har sai an kammala zaben domin wanzuwar zaman lafiya.

Zabe: An zargi 'yan sanda da rashin aiki

A baya mun ruwaito cewa an zargi jami’an yan sanda da biris da aikinsu yayin zaben gwamnan Edo da APC ta samu nasara.

Jam’iyyar PDP ce ta yi zargin, inda ta ce jami’an tsaro na kallo ana cinikin kuri’a a gabansu ba tare da daukar mataki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.