‘Babu Maganar Zabe a 2027,’: Jigon PDP Ya Zargi APC da Shirya Maƙarƙashiya
- Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya zargi jami'yyar APC da yaki da demokradiyya a zaben Edo na ranar Asabar
- Secondus ya ce akwai alamun APC na son lalata dimokuraɗiyyar Najeriya wanda ba lallai a samu karfin gwiwar zaben 2027 ba
- Tsohon shugaban ya kuma yi martani ga Abdullahi Ganduje kan cewa za su yi amfani da tsarin da suka yi a Edo a zabe mai zuwa a Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya yi magana bayan zaben gwamna da ya gabata a jihar Edo.
Uche Secondus ya koka kan cewa sam ba a yi adalci a zaben ba, wanda ya ce hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya.
Vanguard ta wallafa cewa Uche Secondus ya kuma yi martani ga shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon PDP ya nuna fargaba kan zaben 2027
Tsohon shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya ce ba lallai yan jam'iyyar adawa su samu kwanciyar hankalin yin zaɓe a shekarar 2027 ba.
Uche Secondus ya ce jam'iyyar APC ta dauko hanyar lalata dimokuraɗiyya ta yadda ba wani haske da suke gani da za a su iya samu a gaba.
Secondus ya ce ba a yi zabe a Edo ba
Uche Secondus ya ce abin da ya faru a Edo a ranar Asabar ba za a kira shi da zabe ba sai dai kwace mulki kawai.
Shugaban ya ce abubuwan da suke faruwa suna nuna cewa ana cigaba da samun maguɗi ne a zabe maimakon samun gyara.
Tsohon shugaban PDP ya yi martani ga Ganduje
Uche Secondus ya ce maganar da Ganduje ya fada kan cewa za su yi amfani da tsarin zaben Edo a Ondo da Amambra bai dace ba.
Ya kara da cewa hakan na cikin alamun da suke nuna APC ta shirya maguɗi kuma haka za ta yi a shekarar 2027.
Yiaga ta ce an yi magudi a zaben Edo
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin sa-kai masu lura da yadda zaben gwamnan jihar Edo ya gudana a ranar Asabar sun fara fitar da rahoton bayan zabe.
Yiaga Africa ta fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana da kuma kura-kurai da ta ce an tafka a ɓangaren hukumar INEC ta kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng