Damagum: Atiku Ya Tsoma Baki, Ya Faɗi Matsayarsa kan Shirin Sauke Shugaban PDP

Damagum: Atiku Ya Tsoma Baki, Ya Faɗi Matsayarsa kan Shirin Sauke Shugaban PDP

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana goyon bayansa ga shirin tsige shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fara tuntuɓar wasu ƴan kwamitin NWC da ke son Damagum ya bar shugabancin PDP
  • Wannan dai na zuwa ne bayan ƙungiyar gwamnonin PDP ta dare gida biyu kan batun sauke Umar Damagum daga NWC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya goyi bayan shirin tsige muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum.

Bayanai sun nuna cewa Atiku ya fara tuntuɓar ƴan kwamitin gudanarwa (NWC) waɗanda suka fara fafutukar sauke Damagum daga shugabancin jam'iyyar.

Taron PDP.
Atiku ya fata tuntuɓar masu goyon bayan tsige shugaban PDP na ƙasa Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Gwamnonin PDP sun dare gida biyu kan Damagum

Kara karanta wannan

Bayan lallasa PDP a Edo, jam'iyyar APC ta ƙara samun gagarumar nasara a Arewa

Jaridar Punch ta tattaro cewa shirin tsige Umar Damagum ya raba kawunan gwamnoni 13 na na jam'iyyar adawa PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni bakwai karƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi sun haɗa kai, sun matsala lamba kan dole Damgum ya bar muƙaminsa.

Yayin da gwamnoni huɗu karkashin Gwamna Seyi Makinde na Oyo suka nuna gamsuwa da Damagum, sauran gwamnoni biyu kuma sun ce duk inda ta faɗi sha ne, cewar The Nation.

Gwamnonin da suke goyon bayan Damagum ya ci gaba da shugabancin PDP bakinsu ɗaya da ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda alaƙarsa ta yi tsami da ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar.

Atiku da Wike dai sun raba gari gabanin babban zaben 2023, inda Wike ya jagoranci gwamnoni biyar na PDP wajen yaƙar takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Atiku ya fara tuntuɓar ƴan kwamitin NWC

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga taron FEC ana rade raɗin za a kori wasu ministoci, bayanai sun fito

Wani babba a NWC, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin magana da ƴan jarida, ya tabbatar da cewa Atiku ya tuntuɓi wasu daga cikin masu shirin sauke Damagum.

Ya ce:

"Ba mu kadai ba ne, manyan shugabanni a jam’iyyar da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun tuntuɓi wasu daga cikinmu.”
"Ina tabbatar maku da cewa Atiku ya kira wasu daga cikinmu, ya nuna mana ba mu kadai za mu yi yakin ba, kuma yana goyon bayan neman adalci, gaskiya, da daidaito.
“Ba mu da wata matsala da Damagum, burinmu shi ne mu kare jam’iyyar domin ‘yan Nijeriya su samu mafita a zabe mai zuwa. Ya kamata Damagum ya mutunta dokar jam'iyya, ya sauka daga muƙamin."

PDP ta zaɓi sabon shugaba a Kaduna

A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP mai adawa reshen jihar Kaduna ta zabi tsohon kwamishina a matsayin sabon shugabanta.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Manyan jiga jigai 5 da suka yaƙi gwamna, suka kayar da ɗan takarar PDP

Jam'iyyar ta zabi Edward Percy Masha a matsayin shugabanta bayan gudanar da zaben karkashin kulawar ma'aikatan INEC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262