Muhammadu Buhari Ya yi Maganar Zaɓen Edo, Ya Tura Saƙo ga APC da PDP

Muhammadu Buhari Ya yi Maganar Zaɓen Edo, Ya Tura Saƙo ga APC da PDP

  • Hukumar INEC ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ne ya lashe zaben gwamna a Edo na 2024
  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon murna ga dan takarar da ya yi nasara da jami'yyar APC a Najeriya
  • Haka zalika shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira kan yadda za a hadu domin samun nasara da cigaban jihar Edo bayan zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Edo inda dan takarar APC, Monday Okpebholo ya yi nasara.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon taya murna ga jam'iyyar APC kan nasarar da ta samu a zaben.

Kara karanta wannan

Bayan karɓe mulkin Edo, Ganduje ya jero jihohin da APC za ta ƙwace nan gaba

Buhari
Buhari ya yi magana kan zaben Edo. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Garba Shehu ne ya wallafa sanarwa kan abin da Muhammadu Buhari ya fada a shafin tsohon shugaban kasar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya yi murnar lashe zaben Edo

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin ciki kan yadda jam'iyyar APC mai mulki ta lashe zaben gwamna a Edo.

Muhammadu Buhari ya taya dan takarar APC, Monday Okpebholo da jam'iyyar APC murnar samun nasarar.

Buhari ya yi kira ga APC da PDP

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga jam'iyyun da suka fadi zabe musamman PDP kan su hada kai da sabon gwamnan domin kawo cigaba a Edo.

Buhari ya ce hadin kai tsakanin yan takarar zai saka jihar Edo samun nasara wajen haɓaka tattalin arziki.

Zaɓen Edo: Buhari ya yabi jami'an tsaro

Muhammadu Buhari ya yabi jami'an tsaro kan yadda suka tabbatar da zaben Edo ya gudana lami lafiya.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

A karshe, shugaba Buhari ya yi fatan Najeriya ta cigaba da samun nasara da cigaba a karkashin dimokuraɗiyya.

PDP ta yi korafi kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben da su ka fito daga kananan hukumomi biyu a jihar.

Jami'in PDP da ke ofishin INEC, Osagbovo Iyoha ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da hada kai da jam'iyyar APC a kan zaben.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng