Edo: Yayin da Ake Sako Sakamakon Zabe, Gwamnonin APC Sun Koma ga Allah a Bidiyo

Edo: Yayin da Ake Sako Sakamakon Zabe, Gwamnonin APC Sun Koma ga Allah a Bidiyo

  • Gwamnonin APC sun fara murna tun kafin sanar da sakamakon zaben jihar Edo a hukumance yayin da ake cigaba da tattarawa
  • An gano gwamnonin jihohin APC sun dukufa da addu'o'i da kuma murna yayin da ake sako sakamakon zaben
  • Wannan na zuwa ne bayan PDP ta fara korafi kan yadda lamura ke gudana inda ta ce ba ta gamsu da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Yayin da ake dakon sakamakon zaben jihar Edo, gwamnonin jihohin APC sun koma ga Ubangiji.

An gano gwamnonin suna addu'o'in godiya ga Ubangiji yayin da ake cigaba da sake sakamakon zabe a jihar.

Gwamnonin APC sun fara murnar lashe zabe a Edo
Ba a gama sanar da sakamakon zaben Edo ba, gwamnonin APC sun barke da murna. Hoto: All Progrssives Congress.
Asali: Twitter

Edo: Gwamnonin APC sun fara murna

Kara karanta wannan

Edo 2024: Zanga zanga ta barke kan sakamakon zabe, an samu bayanai

Punch ta wallafa wani faifan bidiyo a shafin X inda aka gano gwamnonin sun dukufa addu'o'i a birnin Benin City da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dapo Abiodun shi ya jagoranci sauran gwamnonin a dakin tattara sakamakon zabe na APC a Benin City.

Sauran gwamnonin sun hada da Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos da kuma Lucky Aiyedatiwa na Ondo da sauransu.

Edo: An sanar da wasu sakamakon zabe

Hukumar zabe ta INEC ta fara sake sakamakon zaben da aka gudanar a jiya Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

Akalla an sake sakamakon zaben kananan hukumomi 16 daga cikin 18 da suke fadin jihar.

Wannan na zuwa ne bayan dan takarar gwamnan a PDP, Asue Ighodalo ya nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro suke cafke magoya bayan PDP.

Ighodalo ya koka kan yadda aka samu jinkirin samar da kayayyakin zabe a wuraren da ya fi karfi da al'umma.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: PDP, APC na zaman dari dari bayan INEC ta gaza fara tattara sakamako

Magoya bayan PDP sun fara zanga-zanga a Edo

Kun ji cewa magoya bayan jam'iyyar PDP sun fara zanga-zanga game da zaben gwamnan jiha da ake yi a Edo saboda matsaloli

Jam'iyyar ta nuna damuwa tun farkon zaben kan yadda lamura ke tafiya ba tare da tsari ba inda ta yi fatali da sakamakon

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 10 daga cikin 16 da APC ke kan gaba

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.