'Dan Acaba Ya Lashe Kujera a APC da Aka Fadi Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi

'Dan Acaba Ya Lashe Kujera a APC da Aka Fadi Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi

  • Bayan kammala zaben kananan hukumomi a jihar Kwara, Hukumar zabe ta sanar da sakamakon zabe da aka gudanar
  • Shugaban hukumar zaben jihar (KWSIEC), Mohammed Baba-Okanla shi ya sanar da sakamakon zaben da safiyar yau Lahadi
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zaben a jiya Asabar 21 a watan Satumbar 2024 a kananan hukumomi 16

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Hukumar zaben jihar Kwara (KWSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi.

Hukumar ta ce jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta yi nasarar lashe duka kujerun kananan hukumomi 16.

APC ta lashe zabukan kananan hukumomi a jihar Kwara
Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 16 a jihar Kwara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kwara: INEC ta fadi sakamakon zabe

Shugaban hukumar a jihar, Mohammed Baba-Okanla shi ya tabbatar da haka da safiyar yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton TVC.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke sakamakon zaben Edo da aka dora a IReV

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baba-Okanla ya ce APC ta lashe duka zaben kananan hukumomi 16 da kujerun kansiloli 193 a jihar.

Shugaban ya yabawa jam'iyyu da suka fafata a zaben wurin tabbatar da gudanar da zaben ba tare da tashin hanakali ba.

Ya kuma ya jinjinawa al'ummar jihar Kwara ganin yadda suka fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'u, Tribune ta ruwaito.

Jam'iyyun da suka fafata a zaben jihar Kwara

Sanarwar ta ce daga cikin jam'iyyun da suka fafata a zaben sun hada da APC da PDP da SDP da kuma jam'iyyar Accord.

"Zaben da aka gudanar a kananan hukumomi 16 da gundumomi 193, jam'iyyu biyar ne suka fafata a cikinsa."
"Jam'iyyun da suka shiga zaben a jiya Assbar sun hada da APC da PDP da SDP da APM da kuma jam'iyyar Accord."

- Mohammed Baba-Okanla

Dan Acaba ya samu tikitin takara

Kara karanta wannan

IREV: Ana daf da kammala daura kuri'un zaben Edo, an kusa sanin sabon gwamna

Kun ji cewa Tsohon kansila a jihar Kwara ya samu tikitin tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da za a yi a watan Satumbar 2024.

APC ta gabatar da Abdulazeez Jimoh wanda shi ne shugaban kungiyar yan acaba na tsawon lokaci a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da jihar ke shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.