Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba Masu Kada Kuri'a Cin Hancin N10000’

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba Masu Kada Kuri'a Cin Hancin N10000’

  • Kungiyar Yiaga Africa ta zargi wakilan jam'iyyar PDP da APC da ba masu kada kuri'a toshiyar N10,000 domin su zabi 'yan takararsu
  • Yiaga Africa ta nuna damuwarta kan yadda ta ce an samu rahotannin sayen kuri'u da sauran laifuffukan zabe a zaben jihar Edo
  • Duk da haka, kungiyar ta jinjinawa hukumar EFCC da sauran jami'an tsaro kan cafke wadanda aka kama suna sayen kuri'u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Kungiyar Yiaga Africa ta yi ikirarin cewa zaben gwamnan jihar Edo na cike da sayen kuri'u da sauran laifuffukan zabe inda ake ba masu kada kuri'a cin hancin N10000.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke sa ido kan yadda ake gudanar da zaben jihar Edo daga kowacce karamar hukuma.

Kara karanta wannan

Edo 2024: INEC ta tsawaita lokutan zabe, ta fadi musabbabin ɗaukar matakin

Yiaga Africa ta zargi wakilan APC da PDP da sayen kuri'u a zaben gwamnan Edo
Zaben Edo: Yiaga Africa ta yi magana kan sayen kuri'u da aka kama wakilan PDP, APC na yi. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

An zargi PDP, APC da sayen kuri'u

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Yiaga Africa ta fitar dauke da sa hannun Dakta Aisha Abdullahi, shugabar tawagar kungiyar a zaben Edo, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wakilanmu sun ba mu rahoton cewa an samu sayen kuri'u a kananan hukumomin Ikpoba/Okha, Igueben da Esan ta Yamma.
Sauran kananan hukumomin sun hada da Akoko Edo, Owan ta Yamma da Uhunmode inda aka ga wakilan PDP da APC na ba masu zabe cin hancin N10,000."

- A cewar sanarwar.

Sanarwar ta ce an kama wakilan na aikata wannan laifi ne a rumfar zaben da ke cikin makarantar firamare ta Igueben-Idumoka (12-10-03-004) a karamar hukumar Igueben.

Edo: Yiaga ta jinjinawa EFCC

Sanarwar ta cei gaba da cewa an kuma ga wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a toshiyar N10,000 a rumfar zaben Enikaro- Enikaro a gundumar Ugbekun, da ke Ikpoba/Okha.

Kara karanta wannan

Edo 2024: PDP ta fara korafi, dan takara ya fadi makircin da APC ta shirya

Kungiyar Yiaga Africa ta yabawa hukumar EFCC da jami’an tsaro bisa matakin gaggawar da suka dauka na kame wadanda ake zargin sun sayi kuri’u a rumfunan zabe a kananan hukumomin Egor da Oredo.

Sanarwar ta ce, ya zuwa karfe 1:40 na rana, cibiyar bayanai ta Yiaga Africa WTV ta samu wasu rahotanni masu matukar muhimmanci guda 16 da suka shafi lattin fara kada kuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.