“Tunaninsa Ya San Komai, bai Jin Shawara”: An Fadi Ainihin Halin Tinubu

“Tunaninsa Ya San Komai, bai Jin Shawara”: An Fadi Ainihin Halin Tinubu

  • Sanata Kofowola Bucknor-Akerele ta koka kan irin halin Shugaba Bola Tinubu na rashin karbar shawara
  • Bucknor-Akerele wacce ta rike muƙamin mataimakiyar Tinubu lokacin yana gwamnan Lagos ta koka kan halin da ake ciki
  • Sanatar ta ce abin takaici ne yadda shugaban bai karbar shawara inda ta ce gani ya ke yi ya san komai a rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Tsohuwar mataimakiyar Bola Tinubu a jihar Lagos, Kofowola Bucknor-Akerele ta bayyana halin shugaban kasar.

Bucknor-Akerele ta nuna damuwa yadda Tinubu ke gudanar da mulki duk da kokarin da ya yi a jihar Lagos.

Na hannun daman Tinubu ta ce shugaban bai jin shawara ko kadan
Tsohuwar mataimakiyar Bola Tinubu a jihar Lagos ta koka kan halin shugaban. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kofowola Bucknor-Akerele.
Asali: Facebook

Ta kusa da Tinubu ta fadi halinsa

Kara karanta wannan

"Ba maganar kwasar kudi ba ne": Tinubu ya fadi dalilin zuwansa 'Aso Rock'

Sanatar ta bayyana haka ne yayin hira da jaridar Tribune a yau Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bucknor-Akerele ta ce kwata-kwata Tinubu bai jin shawarar mutane saboda gani ya ke yi ya san komai bai bukatar gyara.

Ta koka kan yadda abubuwa suka tabarbare musamman ta bangaren tsaro a Najeriya.

Shin Tinubu na karbar shawara daga mutane?

"Ba na tsammanin Tinubu yana bukatar shawara ta, ina ga mutum ne wanda bai jin shawarar mutane."
"Na taba zama mataimakyarsa, ba na tsammanin mutum ne mai son shawara, yana da wani irin hali cewa ya san komai."

- Kofowola Bucknor-Akerele

Kofowola Bucknor-Akerele ta rike muƙamin mataimakiyar Bola Tinubu lokacin da ya ke gwamnan Lagos daga 1999 zuwa 2022.

Dattijuwar ta bukaci Bola Tinubu ya duba halin da kasar ke ciki wurin zaban mutane masu kwarewa da za su rika ba shi shawara.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Tinubu ya iske a ofis da suka hana shi zuwa taron Majalisar dinkin duniya

"Na san kuna cikin yunwa" - Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya sani ana cikin wani hali a Najeriya inda ya zargi gwamnatocin baya.

Tinubu ya ce dukan wannan hali da aka shiga na da nasaba da matakan da gwamnatocin baya suka dauka a baya da tsare-tsarensu.

Shugaban ya bukaci hadin kai daga masu ruwa da tsaki da sauran alumma domin ciyar da Najeriya gaba wurin gogayya da sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.