Zaben Edo: Dan Takarar PDP Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara da Gagarumin Rinjaye
- Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Edo ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
- Asue Ighodalo ya nuna ƙwarin gwiwar cewa shi ne zai samu nasara a zaɓen idan har ba a tafka maguɗin zaɓe ba
- Ɗan takarar na PDP ya bayyana cewa bayanan da yake samu sun nuna cewa nasara ta shi ce a zaɓen gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo, Asue Ighodalo ya ce shi ne zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaɓen.
Asue Ighodalo ya bayyana hakan ne bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓensa da ke makarantar firamare ta Indinrio a Okaigben Ewohomi cikin ƙaramar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas ta jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust rahoto cewa Asue Ighodalo ya kaɗa ƙuri'ar ne tare da matarsa, Ifeyinwa Ighodalo da ƙaninsa, Fasto Ituah Ighodalo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asue Ighodalo ya hango nasara a zaɓen Edo
Da yake magana da ƴan jarida, ɗan takarar gwamnan na PDP ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar yin nasara idan ba a yi maguɗi a zaɓen ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Asue Ighodalo ya kuma yabawa jami'an sojoji kan yadda suka samar da tsaro a lokacin zaɓen.
"Ina jin jita-jita cewa suna son murɗe zaɓen, amma bisa ga bayanan da nake samu, jam'iyyar PDP ce za ta lashe zaɓen.
"Zan kira wanda ya yi nasara a zaɓen idan an yi zaɓe na gaskiya da adalci, amma nine wanda za a kira."
- Asue Ighodalo
Oshiomole ya magantu kan zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomole, ya yi magana kan zargin APC ta shirya siyan ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar.
Adams Oshiomole ya musanta zargin cewa jam'iyyar ta tanadi tulin kuɗi domin amfani da su wajen siyan ƙuri'u a hannun mutane a lokacin zaɓen.
Asali: Legit.ng
