Zaben Edo: Jami'an Hukumar EFCC Sun Cafke Masu Sayen Kuri’u, Bayanai Sun Fito

Zaben Edo: Jami'an Hukumar EFCC Sun Cafke Masu Sayen Kuri’u, Bayanai Sun Fito

  • Akalla mutane uku da ake zargi da aikata laifuffukan zabe sun shiga hannun hukumar EFCC yayin gudanar da zaben gwamnan Edo
  • Jami’an EFCC sun bazama zuwa dukkanin kananan hukumomin Edo domin magance sayen kuri'u ko ingiza masu kada kuri’a a zaben
  • A cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta gani, jami'an EFCC sun cafke wasu da ake kyautata zaton masu siyan kuri'a ne a Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC sun cafke wasu da ake zargin suna sayen kuri’u a zaben gwamnan jihar Edo da ke gudana.

Legit Hausa ta ruwaito kamen dai ya faru ne a yankin karamar hukumar Egor, bayan da EFCC ta lashi takobin dakile yunkurin sayen kuri’u da laifuffukan da suka shafi zabe a jihar.

Kara karanta wannan

"Ko nawa ne": Kwamishinar zabe a Edo ta magantu kan karbar rashawa, ta fadi shirinta

Jami'an hukumar EFCC sun cafke masu sayen kuri'u a zaben jihar Edo
Edo: Hukumar EFCC ta cika hannu da wasu mutane uku da ake zargin suna sayen kuri'u.
Asali: Twitter

Zaben Edo: EFCC ta yi kame

Rahoton da Channels TV ta fitar ya nuna cewa hukumar ta kama mutanen ne a gunduma ta 7, karamar hukumar Egor da ke jihar ta Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika an ruwaito cewa jami’an EFCC sun tafi da mutanen ukun da suka kama da suka hada da maza biyu da mace daya.

Sai dai an ce wasu mutane da ke a wajen sun nuna adawa da kama mutanen da EFCC ta yi, inda suka dage cewa ana cin zarafinsu ne.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Duba labarai kan zaben Edo a kasa:

Rigima ta barke a rumfar zabe, INEC ta manta da takardar rubuta sakamako

KAI TSAYE: Yadda zaben gwamnan jihar Edo ke gudana

Zaben Edo: Dan takarar jam'iyyar APC, Okpebholo ya kada kuri'arsa

Laifuffukan zabe a kundin mulki

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya jawo jam'iyyar PDP ta faɗi a zaɓen gwamnan jihar Edo

Tun da fari, mun ruwaito cewa ba da kudi ga masu kada kuri’a, ko jawo ra'ayin masu kada kuri’a a wata haramtacciyar siga ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya kan zabe.

Hakazalika, mun tattaro maku wasu manyan laifuffukan zabe da idan aka kama mutum ya aikata su ka iya kaishi ga gidan yari ko cin tara mai yawa ko kuma duka biyun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.