"Babu Makawa": Jigon APC Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaben Gwamnan Edo
- Wani jigo a jam'iyyar APC, Francis Okoye ya yi hasashen cewa ɗan takarar jam'iyyar, Sanata Monday Okpebholo, zai lashe zaɓen gwamnan jihar Edo
- Francis Okoye ya bayyana cewa babu yadda za a yi ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo ya yi nasara a kan Okpebholo
- A yayin wata tattaunawa da Legit.ng, ya bayyana dalilan da za su sanya APC da ɗan takarar ta za su lashe zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Wani jigon jam’iyyar APC, Francis Okoye, ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan jihar Edo wanda za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.
Francis Okoye ya ce babu makawa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, zai kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo.
Jigon na APC ya ce tasirin Adams Oshimole da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, zai taimakawa APC a zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Juma’a, 20 ga watan Satumba.
Dalilin da yasa APC za ta lashe zaɓen gwamnan Edo
"A nawa ra'ayin za mu ci zaɓe, APC ta yi duk shirin da ya dace. Adams Oshiomole da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ƴan siyasa ne na asali."
"Waɗannan jiga-jigan guda biyu sun fito ne daga mazaɓar sanatan da ke da mafi yawan masu kaɗa ƙuri'a a jihar Edo."
- Francis Okoye
Ya ƙara da cewa alamomi daga wajen yaƙin neman zaɓe sun nuna cewa mutanen Edo za su kaɗa ƙuri’a ga jam’iyyar APC a ranar Asabar 21 ga watan Satumba.
APC za ta lashe kujerar gwamnan Edo
Francis Okoye ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Okpebholo ne zai lashe kujerar gwamna bayan ya samu mafi yawan ƙuri’u.
"Idan muka dubi alamomi daga wajen kamfen, za ku ga cewa jama’a za su yi APC ne, saboda haka babu yadda za a yi APC ba za ta lashe kujerar ba a ranar Asabar ɗin nan."
"Saboda haka ina fatan nasara tamu ce kuma za mu yi nasara. Domin haka, babu wata makawa, Edo APC ce, kuma APC Edo ce."
- Francis Okoye
Ƴan sanda sun yi gargaɗi kan zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi gargaɗi kan zaɓen gwamnan jihar Edo na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
Rundunar ƴan sandan ta buƙaci mutanen da suka fito domin kaɗa ƙuri'a da su koma gidajensu da zarar sun kammala yin zaɓe.
Asali: Legit.ng