Hanyoyin da INEC Ke Bi wajen Tabbatar da Dan Takarar da Ya Lashe Zaben Gwamna a Najeriya
- Mutane da dama ba su da masaniya kan hanyoyin da ake bi kafin a samu ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamna a Najeriya
- Wasu za su yi tunanin cewa ɗan takarar da ya samu mafi yawan ƙuri'u kaɗai shi ne wanda ake bayyanawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna
- Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi sharuɗa guda biyu waɗanda dole sai an cika su kafin a bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Zaɓen gwamna na ɗaya daga cikin zaɓuɓɓukan da ake gudanarwa a Najeriya domin zaɓar shugabannin da za su jagoranci al'umma
Gwamnoni dai a Najeriya su ne suke da iko tare da alhakin jan ragamar jihohin da suke mulka a Najeriya.
Ana gudanar da zaɓen gwamnoni ne domin zaɓar mutanen da za su ja ragamar jihohi da ke tarayyar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaɓen na gwamnoni dai ana gudanar da shi ne a dukkanin rumfunan zaɓe na mazaɓu da ƙananan hukumomin jiha.
Bayan kammala kaɗa ƙuri'a, abu na gaba shi ne bayyana ɗan takarar da ya samu nasara a wannan zaɓen da aka gudanar.
Hanyoyin samun wanda ya lashe zaɓen gwamna
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi bayani filla-filla kan hanyoyin da ake bi wajen samun ɗan takarar da ya samu nasara a zaɓen gwamna, cewar rahoton tashar Channels tv.
Mutane da yawa za su yi tunanin cewa ɗan takarar da ya samu yawan ƙuri'u kaɗai a zaɓen gwamna shi ne wanda ake bayyanawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Sai dai ba haka lamarin yake ba.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya samar da sharuɗa guda biyu waɗanda dole sai an cika su kafin samun ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamna.
1. Samun yawan ƙuri'u
Ɗaya daga cikin sharaɗin lashe zaɓen gwamna kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadi, shi ne samun mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen.
Hakan na nufin cewa kafin a bayyana ɗan takara a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna, dole ne ya samu ƙuri'u mafi yawa da aka kaɗa a zaɓen.
2. Samun kaso 1/4 na ƙuri'u a ƙananan hukumomi
Sharaɗi na biyu da dole sai ya cika kafin a bayyana wanda ya lashe zaɓen gwamna shi ne sai ya samu kaso 1/4 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa a aƙalla kaso 2/3 na ƙananan hukumomin jihar, cewar rahoton Premium Times.
Misali a jihar da ke da ƙananan hukumomi 20, dole ne ɗan takarar ya samu kaso 25% na ƙuri'un da aka kaɗa a aƙalla ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Idan aka kasa cika sharuɗan fa?
Yana iya yiwuwa a zagaye na farko na zaɓen ba a samu ɗan takarar da ya cika waɗannan sharuɗan guda biyu na samun mafi yawan ƙuri'u da kaso 1/4 na ƙuri'un da aka kaɗa a kaso 2/3 na ƙananan hukumomin jihar.
Idan aka samun hakan, kundin tsarin mulki ya yi tanadin hukumar zaɓe ta INEC ta shirya zaɓe zagaye na biyu a cikin kwanaki 21.
Wanda zai lashe zaɓen gwamnan Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto na cocin The Lord Grave Provinces, da ke birnin Umuahia a jihar Abia, Prophet Joel Atuma ya ce "ɗan takarar da aka raina" a zaben gwamnan jihar Edo na 2024 ne zai lashe zaben.
A cikin wani faifan bidiyo, malamin addinin ya bayyana cewa za a yi shari'a bayan an kammala zaɓen gwamnan Edo.
Asali: Legit.ng