Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci kan Sauya Shekar Ƴan Majalisa 27

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci kan Sauya Shekar Ƴan Majalisa 27

  • Kotu ta kori ƙarar da aka nemi maye gurbin ƴan majalisar dokoki 27 da ke goyon bayan Nyesom Wike a rikicin jihar Ribas
  • Jam'iyyar APP ta kai ƙarar ƴan majalisar dokokin bisa sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa APC, inda ta nemi a maye gurbinsu
  • Kotun ta yi watsi da ƙarar nan take, ta ce masu shigar da ƙarar sun saɓawa tsarin shari'a saboda an riga an yi hukunci kan ƙorafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ƙarara da aka nemi maye gurbin ƴan majalisar dokokin jihar Ribas 27 masu goyon bayan Nyesom Wike.

Tun farko masu shigar da ƙarar sun bukaci kotun ta tabbatar da sauke ƴan majalisar saboda sun sauya sheka daga PDP zuwa APC tare da ba da damar maye gurbinsu.

Kara karanta wannan

Kumallon mata: Wata matar aure a Kano ta zuba 'fiya fiya' a abincin ɗan kishiyarta

Martin Amaewhule.
Babbar kotun tarayya ta kori ƙarar da ake nemi maye gurbin ƴan majalisar tsagin Wike a Ribas Hoto: Martin Amaewhule
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke a rikicin Ribas?

Da yake yanke hukunci yau Jumu'a, Mai Shari'a Peter Lifu na babbar kotun tarayya ya kori ƙarar bisa dalilai da dama, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Lifu ya ce karar da jam’iyyar APP ta shigar ta saɓawa tanadin doka kuma ba a shigar da ita cikin kwanaki 14 da doka ta amince ba.

Legit Hausa ta gano cewa ƴan majalisar sun sauya sheƙa zuwa APC ne a watan Disamba, 2023, ita kuma APP ta kai ƙarar ne watanni takwas bayan nan a watan Yuli, 2024.

APP ta saɓawa tsarin shari'a - Kotu

Bayan haka, Alkalin ya ce ƙarar da APP ta shigar cin mutuncin tsarin shari'a ne saboda an shigar da kararraki da dama kan batun sauya sheƙar ƴan majalisar a kotun.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya 'kashe' budurwar da zai aura Naja'atu Ahmad a jihar Kano

Sannan ya karanto wani hukuncin da babbar kotun ta yanke a baya kan ƙorafin, inda ta yi watsi da buƙatar maye gurbin ƴan majalisar saboda babu ƙwararan shaidu.

Mai shari'a Lifu ya ce tun da ba a soke wannan hukunci ba kuma babu wanda ya ɗaukaka ƙara, hukuncin na nan daram kan sauya shekar ƴan majalisar su 27, in ji Premium Times.

Wike ya gana da ƴan BoT

A wani rahoton kuma ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya gana da ƴan majalisar amintattu na PDP (BoT) a daren ranar Talata, 17 ga watan Satumba 2024.

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan taro wani wani ɓangare ne a yunƙurin BoT na kawo ƙarshen rigimar siyasar da ta dabaibaye jihar Ribas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262