Ana Gobe Zaben Edo, Jonathan Ya Tura Muhimmin Sako ga INEC da Jami’an Tsaro
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan zaben gwamna da ake shirin gudanarwa a jihar Edo
- Jonathan ya bukaci a tabbatar da adalci, a ba mutane yancin zaben wanda suke so da tabbatar da tsaron rayuka yayin zaɓen
- A gobe Asabar, 21 ga Satumba hukumar zabe mai zaman kanta za ta gudanar zaben gwamna a Edo da ke kudancin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Yan Najeriya na cigaba da bayani kan zaben gwamnoni da za a gudanar a jihar Edo a gobe Asabar.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga hukumomi kan tabbatar da gaskiya yayin zaben.
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaba Jonathan ya ce yin gaskiya yayin zaben na cikin girmama dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Edo: Jonathan ya yi kira ga yan siyasa
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga yan siyasa kan bin doka da oda yayin da za a gudanar da zaben gwamna a jihar Edo.
Tribune ta wallafa cewa Goodluck Jonathan ya ce ka da su dauki zaben a matsayin ko a mutu ko a yi rai, ya ce duk abin da za su yi su tabbatar yana cikin doka.
Goodluck Jonathan ya yi kira ga jami'an tsaro
Shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira na musamman ga jami'an tsaro kan tabbatar da ba su muzgunawa masu zabe ba.
Ya kuma bayyana cewa akwai matuƙar bukata ka da jami'an tsaro su nuna wariya ga wata jam'iyya domin hakan karya doka ne.
Kiran Jonathan ga INEC a zaben Edo
Goodluck Jonathan ya ce yana da muhimmanci sosai hukumar INEC ta tabbatar da adalci a kan harkar zaben baki daya.
Ya ce rashin adalci daga INEC na haifar da rikicin bayan zabe, kin yin zaɓe a gaba da rikicin siyasa a cikin kasa.
Zaben Edo: Dokokin zabe a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta shirya tsaf domin sake gudanar da zaben gwamna a jihar Edo a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.
Legit ta tara bayanai domin sake tunatar da ‘yan Najeriya dokokin da ke hana aikata laifuffukan zabe da katsalandan ga tsarin gudanar da zaben.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng