PDP Ta Dare Gida Biyu, Sabon Shugaban Jam'iyya Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Arewa

PDP Ta Dare Gida Biyu, Sabon Shugaban Jam'iyya Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki a Arewa

  • Abubuwan sun kara dagulewa a jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina bayan Yakubu Lado da Mustapha Inuwa sun raba gari
  • Tsagin PDP karƙashin Sanata Yakubu Lado ya rantsar da sababbin shugabannin jam'iyya bayan kammala taruka a faɗin jihar
  • Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya ja tawagarsa, ya ce za su nemi haƙƙinsu a gaban alkali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kastina - Rigingimun cikin gida a jam'iyyar PDP reshen Katsina sun kara tsanani da tsohon ɗan takarar gwamna, Yakubu Lado ya tabbatar da tsaginsa.

Tsagin PDP da ke ƙarƙashin jagorancin Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya naɗa sababbin shugabannin jam'iyya, lamarin da ya ƙara hargitsa jam'iyyar adawa.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina a Kaduna ya zama shugaban PDP, ya shirya ɗaiɗaita APC

Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum.
Rikicin PDP ya ƙara tsanani a jihar Katsina, Yakubu Lado da Mustapha Inuwa sun raba gari Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, ɓangaren Yakubu Lado ya rantsar da Alhaji Nura Amadi Kurfi a matsayin sabon shugaban PDP na Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta rantsar da sabon shugaba a Katsina

An gudanar da bikin rantsuwar ne a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke cikin garin Katsina bayan kammala tarukan zaɓen shugabanni.

Alhaji Nura Kurfi ya yabawa shugabancin PDP na kasa da kuma Sanata Yakubu Lado bisa yadda suka jagoranci jam'iyyar ta samu nasararo a wasu zaɓukan 2023.

Ya bayyana abubuwan da zai mayar da hankali a kai da suka hada da haɗin kai, bin doka da oda, zaman lafiya a cikin gida da ba kowa dama a zaben 2027.

PDP: Mustapha Inuwa ya yi fatalin da tsagin Lado

Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, ya ja na shi tawagar a PDP.

Kara karanta wannan

Kano: PDP na tsaka da kokarin warware rikicinta, 'yan jam'iyyar sun koma APC

Dr. Mustapha Inuwa ya nuna damuwarsa kan yadda aka yi fatali da tsaginsa a gangamin zaɓen shugabannin jam'iyya da aka yi, ya ce zai shigar da ƙara kotu.

Sai dai a ɓangaren da Lado ke jagoranta, sun gudanar da gangamin taron tun daga matakin gunduma, ƙananan hukumomi da jiha inji rahoton Daily Post.

Wani ɗan PDP a Katsina, Usman Suleiman ya shaidawa Legit Hausa cewa ba wani rabuwa da jam'iyyar ta yi a Katsina.

Usman, wanda ke tare da tsagin Lado, ya ce uwar jam'iyya na ƙasa ta san da zaman zaɓen da aka yi, don haka ba zasu bari wani ya kawo masu rabuwar kai ba.

"Mu kanmu a haɗe yake babu wani darewa da PDP ta yi a Katsina, kowa ya san Lado ne jagora, shi Mustapha Inuwa mulki yake so shiyasa zaɓen bai masa daɗi ba," in ji shi.

Wasu ƴan PDP da NNPP sun koma APC

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da wani shugaban al'umma

A wani rahoton kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya karbi sababbin masu tuban siyasa da su ka koma jam'iyyarsa ta APC.

A ziyarar da su ka kai wa Barau har Abuja, wasu 'yan PDP, NNPP da mata masu tafiyar Kwankwasiyya sun bar siyasar iyayen gidansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262