EFCC vs Yahaya Bello: Tsohon Gwamna Ya Sake Tserewa Hukuma kan Zargin Rashawa
- Zuwa yanzu dai ba a san lokacin da wasan 'yar buya tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai kare ba
- A baya bayan nan, an samu ja-in-ja tsakanin EFCC da Yahaya Bello kan ikirarin amsa gayyatar hukumar da tsohon gwamnan ya ce ya yi
- EFCC da ta mamaye gidan da Yahaya Bello ke buya a Abuja ta gaza kama shi a karo na biyu inda a yanzu ba a san inda ya ke ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Har yanzu dai ana ci gaba da yin wasan 'yar buya tsakanin hukumar EFCC da kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Yahaya Bello.
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka ce EFCC ta gaza cafke Yahaya Bello a daren Laraba bayan mamaye gidan gwamnatin Kogi da ke Asokoro.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a gidan gwamantin Kogi na Asokoro ne tsohon gwamnan jhar, Yahaya Bello ya boye kansa daga kamun hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya Bello na boyewa hukumar EFCC
Kafin daren ranar Laraba, lokacin da jami'an hukumar dauke da makamai suka mamaye gidan, tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa ya amsa gayyatar EFCC.
Yahaya Bello ya yi ikirarin cewa ya dainda boye boye kan zarge-zargen da ake yi masa kasancewar shi mai gaskiya ne, don haka zai mika kansa.
A lokacin da ya yi ikirarin, an ce ya na zaune ne a gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Lokoja, inda ya boye kansa kafin daga bisani ya garzaya Abuja domin amsa gayyatar EFCC.
Gwamnan Kogi ya ba Yahaya Bello mafaka
Majiya da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa bayan shafe awanni da mamaye gidan gwamnatin Kogi na Asokoro, jami'an EFCC sun gaza kama Yahaya Bello.
Majiyar daga hukumar EFCC ta yi nuni da cewa gwamnan jihar Kogi ne ya ke ba tsohon gwamnan kariya, lamarin da ya sa jami'an suka gaza kama shi.
“Ba don magajinsa ba, gwamna mai ci da ke ba shi mafaka ai da tuni mun kama shi. Wannan kuwa ya yi daidai da umarni kotu na cafke shi."
- A cewar majiyar.
Ya zuwa yanzu dai majiyar ta ce ba a san inda tsohon gwamnan na Kogi ya shiga ba, amma dai EFCC ta sauya salo kuma tana ci gaba da farautarsa.
Yahaya Bello ya fada hannun EFCC?
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar ta EFCC ta bakin kakakinta, Dele Oyewale, ta yi karyata cewa ta aika gayyata ga Yahaya Bello, mutumin da take nema ruwa a jallo.
Hukumar ta bayyana cewa tsohon gwamnan na Kogi, Yahaya Bello ba ya hannunta kuma tana ci gaba da nemansa kan zargin karkatar da Naira biliyan 80.2.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng