Edo 2024: Jerin Yawan Jihohin da APC, PDP da NNPP Ke Mulki a Najeriya

Edo 2024: Jerin Yawan Jihohin da APC, PDP da NNPP Ke Mulki a Najeriya

Bayan kammala zaben watan Maris din 2023, jam'iyyu daban-daban sun yi nasarar lashe takara a jihohin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Daga bisani jihohin Kogi da Imo da Bayelsa sun yi zabe a watan Nuwambar 2023 inda APC ta samu jihohi biyu sai kuma PDP ta tashi da daya.

Jihohin da APC da PDP da kuma NNPP ke mulkinsu a Najeriya
Yawan jihohin da APC da PDP da kuma NNPP ke jagoranta a Najeriya. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dauda Lawal, Uba Sani.
Asali: Facebook

A wannan shekara ta 2024, za a yi zabe a jihar Edo a ranar Asabar 21 ga watan Satumba yayin da a watan Nuwamba za a yi na Ondo.

Legit Hausa ta duba muku jihohin da jam'iyyu daban-daban ke mulki da suka hada da APC da PDP da LP da NNPP da APGA daga shafin Wikipedia.

Kara karanta wannan

Kano: PDP na tsaka da kokarin warware rikicinta, 'yan jam'iyyar sun koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da APC ke mulki

Gombe

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi nasarar lashe zaben gwamna a hannun PDP a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar APC.

Jigawa

A jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi yana wa'adinsa na farko ne bayan lashe zaben da aka yi a watan Maris din 2023.

Kaduna

Gwamna Uba Sani ya gaji mulkin Kaduna daga hannun Nasir El-Rufai a watan Maris na 2023 karkashin APC.

Ragowar jihohin da ke hannun APC

Sauran sun hada da Benue da Borno da Cross River da Ebonyi da Ekiti da Imo da Katsina da kuma Kebbi.

Sai kuma Kogi da Kwara da Lagos da Nassarawa da Niger da Ogun da Ondo da Sokoto da kuma Yobe.

Jihohin da PDP ke mulki a yau

Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri ya lashe zabe a karkashin jam'iyar PDP a zaben shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N80bn: Yahaya Bello ya faɗi yadda ta kaya bayan ya miƙa kansa ga EFCC

Bauchi

Jihar Bauchi na karkashin mulkin PDP inda Bala Mohammed ke jagoranta tun zaben shekarar 2019 da aka yi.

Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Dare ya kwace mulki daga Bello Matawalle da ke jam'iyyar APC a zaben 2023 da aka gudanar.

Sauran jihohin sun hada da Akwa Ibom da Bayelsa da Delta da Edo da Enugu da Osun da Oyo da Rivers da Plateau da kuma Taraba.

Jihohin da sauran jam'iyyun adawa ke mulki

Kano

Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP ya yi nasarar kayar da gwamnantin APC a zaben watan Maris din 2023 da aka gudanar.

Abia

A jihar Abia kuma, jam'iyyar LP ce ta yi nasara kan PDP a zaben watan Maris din 2023 da aka yi inda Gwamna Alex Otti ke jagoranta.

Anambra

Gwamna Charles Soludo shi ya yi nasarar cin zabe a jam'iyyar APGA a zaben da aka gudanar a 2022.

Jerin yan takara 17 a zaben Edo

Kara karanta wannan

Jiga jigan NNPP a jihohi 5 sun shiga matsala, an fara bincikensu

Kun ji cewa a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024 hukumar zaben ta sanar da cewa za a gudanar da zaben sabon gwamna a jihar Edo.

Wannan rahoto ya binciko muku dukkan yan takara 17 da za su fafata a zaben a jam'iyyu daban-daban domin zama gwamna a bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.