Tsofaffin Ƴan Majalisa da Wasu Kusoshi Sun Koma a APC, PDP Ta Yi Martani
- Wasu manyan kusoshin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, 2024 a jihar Ondo
- Wannan sauya sheƙa dai ya ja hankalin jam'iyyar PDP, inda ta fito tana cewa dama can waɗanda suka koma APC sun zame mata ƙaya
- Kwamitin kamfen PDP ya bayyana cewa masu sauya shekar ba za su tsinanawa APC komai ba face rashin nasara a zaɓe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta ce sauya shekar da wasu jiga-jiganta suka yi zuwa APC bai rage ta da komai ba.
A ranar Laraba ne wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka sanar da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Ondo.
Ondo: Jiga-jigan PDP sun koma APC
Punch ta ce wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar sun hada da tsohon dan majalisar tarayya Mista Akinlaja Joseph, Lad Alaba Ojomo da Victor Akinjo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran kusoshin PDP da suka bi sahu zuwa APC a Ondo sun haɗa da Gboluga Ikengboju da kuma tsohuwar kakakin majalisar dokokin jihar, Jumoke Akindele.
Duk da wannan koma baya, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa babu tantama ɗan takararta ne zai lashe zaben gwamnan da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba a Ondo.
PDP ta mayar da martani kan sauya shekar
Mai magana yawun kwamitin kamfen ɗan takarar gwamna a PDP, Mr Ayo Fadaka, shi ya mayar da martani kan sauya sheƙar jiga-jigan a wata sanarwa.
A cewar sanarwar, waɗanda suka sauya shekar sun riga sun haɗe da APC tun kafin su sanar da barin PDP, don haka ba wani abin damuwa ba ne, in ji The Nation.
"Mun lura cewa waɗannan mutane ƴan tsalle-tsalle ne daga wannan jam'iyya zuwa wata a duk lokacin da aka ce zaɓe ya matso, ba su iya zama wuri ɗaya.
"Ba za su tsinanawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa da jam’iyyarsa komai ba, maimakon haka za su ƙara masa rashin sa'a, don haka muna taya gwamna da APC murna."
- Ayo Fadaka.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi sabbin naɗe-naɗe
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya sake zaɓo wasu mutane ya ba su muƙamai a gwamnatinsa.
Gwamnan ya naɗa sababbin hadimai mutum 344 waɗanda za su riƙa taimaka masa wajen gudanar da mulkin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng