Tinubu na Shirin Rusa Wata Ma'aikata, An Matsa Masa Lamba Ya Kori Wasu Ministoci

Tinubu na Shirin Rusa Wata Ma'aikata, An Matsa Masa Lamba Ya Kori Wasu Ministoci

  • Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirye-shiryen yin garambawul a majalisar zartaswa domin inganta ayyukan gwamnati
  • Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun ce Tinubu na shirin rusa ma'aikatar jin kai da yaki da fatara, sannan zai kori wasu ministoci
  • Alamu sun nuna Shugaba Tinubu na iya haɗe wasu hukumomi wuri ɗaya, sannan ya raba ayyukan wasu ma'aikatu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alamu masu karfi na nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya rusa ma'aikatar harkokin jin kai da yaki da talauci.

Wannan dai na ɗaya daga cikin abubuwan da ake tsammanin shugaban kasar zai yi idan ya tashi garambawul a majalisar zartaswa ta gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shririn yin garambawul a gwamnatinsa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa Punch cewa da yiwuwar Tinibu ya rarraba wasu ma'aikatun kuma ya dunƙule wasu hukumomi wuri ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An matsawa Tinubu ya kori wasu ministoci

Haka nan kuma majiyar ta ce shugaba Tinubu na iya korar wasu daga cikin ministocinsa duk a wani ɓangare na yiwa gwamnatinsa kwaskwarima.

Bola Tinubu dai na fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC kan cewa ya kamata ya sallami ministocin da suka gaza taɓuka komai.

Duk da cewa shugaban kasar ya yi gargadin cewa ba zai lamurci gazawa daga ministoci ba kimanin watanni 10 da suka gabata, har yanzun dai bai taɓa kowa ba.

Wane gyara Bola Tinubu ke shirin yi?

A halin yanzu, wasu majiyoyi a fadar shugaban ƙasa sun ce babu shirin sauyawa wasu ministoci wurin aiki, maimakon haka Tinubu zai raba ko ya haɗe wasu ma'aikatun.

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

Wani jami'an gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da yiwuwar a rushe ma'aikatar jin kai bayan dakatar da Dr. Betta Edu tun a watan Janairu.

"Ina tunanin an ƙara samun jinkiri, hasali ma a makon jiya ya kamata (Tinubu) ya sanar da sauye-sauyen to amma ba ya ƙasar shiyasa.
"Bari na faɗa maku wani abu, shugaban kasa na iya rusa ma'aikatar jin kai saboda yana ganin babu bukatarta a yanzu, akwai hukumomin da suke aikin da take yi," in ji majiyar.

Sarkin Minna ya kare Bola Tinubu

A wani rahoton kuma sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa amma ƴan Najeriya ba su gane ba.

Mai martaba sarkin ya ce gwamnatocin da suka gabata sun talauta Najeriya yayin da Tinubu ke ƙoƙarin kwato kudin da suka sace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262