"In Sha Allahu Za Mu Dinke Ɓaraka," Gwamna Ya Gano Waɗanda Suka Haddasa Rikici a PDP

"In Sha Allahu Za Mu Dinke Ɓaraka," Gwamna Ya Gano Waɗanda Suka Haddasa Rikici a PDP

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya zargi APC da hannu a rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar PDP
  • Sanata Bala Mohammed ya ce burin APC ta tarwatsa PDP amma duk da haka za su lalubo bakin zaren nan ba da jimawa ba
  • Gwamnan ya yi wannan furuci lokacin da ya karɓi bakuncin ƴan majalisar amintattu (BoT) na babbar jam'iyyar adawar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce a sahun gaba wajen hana PDP zaman lafiya.

Gwamna Bala ya ce idan Allah ya so nan ba da daɗewa ba za su lalubo bakin zaren, su ɗinke duk wata ɓaraka a babbar jam'iyyar adawar.

Kara karanta wannan

Olumide Akpata: Dan takarar LP mai barazana ga jam'iyyu a zaben Edo

Wike da Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan Bauchi ya zargi APC da hannu a ruwa wutar rikicin PDP Hoto: @GovWike, @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X jim kaɗan bayan ya karbi baƙuncin ƴan majalisar amintattu na PDP a gidan gwamnati da ke Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala ya gano masu rura wutar rikicin PDP

"Duk wani kalubale yana da mafita, za mu shawo kan matsalar in sha Allahu kuma za mu lalubo bakin zaren. PDP ce kaɗai ke fama da wannan ƙalubale saboda ta na da gogewar mulki.
"Idan ku ka lura ɗaya ɓangaren ne suka jawo mana, ba su son mu zauna lafiya, APC ce ta haɗa mu faɗa a cikin gida, burinsu su samu bara gurbi a cikinmu waɗanda za su kwashi sirrinmu su kai masu.
"Hatta Wike da ya shiga gwamnatin APC ɗan PDP ne, kowa na ganin ƙoƙarin da yake yi, ba su da zaƙaƙuran mutane irin namu shiyasa suka ɗauke shi, suka ba shi wuri kamar jiha da zai jagoranta."

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamnonin PDP sun fara ƙokarin sauya shugaban jam'iyya na ƙasa

- Bala Mohammed.

PDP ta maida hankali kan zaɓen 2027

Gwamna Bala ya alaƙanta rikicin da PDP ke fama da shi da fuska biyun Wike da adawar APC, inda ya ba da tabbacin cewa suna da dabarun da za su warware lamarin.

A cewarsa, babban abin da PDP ta fi mayar da hankali shi ne hada kan jam’iyyar domin kwsce ragamar mulki a 2027 da tabbatar da ingantaccen shugabanci.

Gwamnoni sun juyawa shugaban PDP baya

A wani rahoton gwamnonin PDP sun sanar da cewa za su yi koƙarin maido da kujerar shugaban jam'iyyar yankin Arewa ta Tsakiya kamar yadda doka ta tanada.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana hakan bayan ganawa da 'yan majalisar NWC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262