PDP Ta Gaji da Lamarin Gwamnan Sokoto, Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Kwangilar N30bn

PDP Ta Gaji da Lamarin Gwamnan Sokoto, Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Kwangilar N30bn

  • Yayin da ake surutu kan gyaran bohula a jihar Sokoto, jam'iyyar PDP ta bukaci binciken Gwamna Ahmed Aliyu
  • Jam'iyyar ta yi Allah wadai da sake ware makudan kudi har N30bn domin katange hanyoyi a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya ce zai gyara bohula 25 kan kudi N1.2bn da ake ta maganganu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta bukaci bincikar ayyukan gwamnatin Ahmed Aliyu.

Jam'iyyar ta ce ya kamata hukumar EFCC ta bincike ayyukan N30bn da gwamnan ya ware domin katangar hanya.

PDP ta kalubanci gwamnan Sokoto kan ware wasu N30bn a jihar
Jam'iyyar PDP bukaci EFCC ta binciki gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Twitter

EFCC: PDP ta bukaci binciken gwamna Sokoto

Kakakin jam'iyyar a jihar, Hassan Sahabi Sanyinawal shi ya bayyana haka a yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tambuwal: PDP ta yi martani da aka tabo binciken tsohon gwamna kan satar N16bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanyinawal ya ce kwata-kwata aikin ba shi da fa'ida duba da halin da ake ciki a yanzu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce PDP a shirye take domin bincikar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da ta shude.

Jam'iyyar ta ce tsofaffin mukarraban Tambuwal sun shirya bayyana a gaban kwamitin bincike duk lokacin da ake bukatarsu.

"Mutanen Sokoto ba su gama da batun gyara bohula ba kan N1.2bn, yanzu kuma an ware N30bn domin katangar hanya wanda ba ta da amfani."

- Hassan Sahabi Sanyinawal

Jam'iyyar PDP ta zargi batawa Tambuwal suna

Jam'iyyar ta zargi Gwamna Aliyu da kawar da hankulan al'umma wurin tayar da maganar tsohon gwamnan jihar, Tambuwal.

Ta ce gwamnatin Tambuwal ita ce ta gudanar da mulki cikin gaskiya kuma a bayyane a jihar.

Sokoto: An fara binciken tsohon gwamna, Tambuwal

Kara karanta wannan

An firgita da jin harbe harbe da EFCC suka farmaki Yahaya Bello a Abuja

Kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta waiwayi tsohon gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal inda za ta fara bincikensa kan zargin karkatar da N16.1bn.

Kwamitin shari'ar da aka dorawa alhakin binciken gwamnatin Tambuwal ya ce zai gano inda aka kai kudin hannayen jarin jihar Sokoto.

An rahoto cewa ana zargin Tambuwal ya karkatar da kudin bayan sayar da hannayen jarin jihar a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.