Jiga jigan NNPP a Jihohi 5 Sun Shiga Matsala, an Fara Bincikensu

Jiga jigan NNPP a Jihohi 5 Sun Shiga Matsala, an Fara Bincikensu

  • Rikicin jam'iyyar NNPP ya sake sauya salo bayan kaddamar da fara bincike kan jita-jiganta a jihohi biyar
  • Jam'iyyar ta ce an dakatar da jita-jigan ne a jihohi biyar saboda zargin yi maga zagon kasa da cin amana
  • Sakataren yada labaran jam'iyyar, Ladipo Johnson ya ce jihohin sun hada da Gombe da Bauchi da Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta fara binciken wasu jita-jiganta a jihohi biyar a Najeriya.

Jam'iyyar ta ce ta kaddamar da fara bincike kan mambobin kwamitin zartarwa da aka dakatar kan zargin zagon kasa.

Jam'iyyar NNPP ta fara binciken jiga jiganta a jihohi 5
Jam'iyyar NNPP ta kaddamar da fara binciken jiga jiganta kan zargin zangon-kasa a jihohi 5. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, NNPP.
Asali: Facebook

Zangon-kasa: An fara binciken jiga-jigan NNPP

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

Sakataren yada labaran jam'iyyar, Ladipo Johnson shi ya bayyana haka a yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Johnson ya ce jihohi sun hada da Gombe da Taraba da Bauchi da Oyo da kuma jihar Benue, cewar rahoton Vanguard.

Ya ce NNPP ta dauki matakin ne bayan rusa shugabannin jam'iyyar a matakin jihohi a kwanakin nan.

Idan ba a manta ba, a farkon watan Satumbar 2024 ne aka rusa shugabannin jam'iyyar domin yin garambawul.

"An dauki matakin binciken tsofaffin mambobin kwamitin da kuma sauran yan jam'iyya saboda kokarin kawo gyara a cikinta."

- Ladipo Johnson

NNPP ta jero wasu da aka dakatar

Ladipo ya ce daga cikin wadanda aka dakatar a jihohin akwai Mrs. Ayobami Idowu Adekunle da Alhaji Rasheed Adebisi Olopoeniyan.

Sauran sun hada da Mr. Demola Oke da Mr. Kilamuwaiye Badmus da Mr. Oyesola Ololade da Mr Olayiwola Musibau.

Kara karanta wannan

Olumide Akpata: Dan takarar LP mai barazana ga jam'iyyu a zaben Edo

Sai kuma Mr. Tunde Adedapo, da kuma Ms Riike Olaniran domin kawo sauyi a jam'iyyar da ke adawa a kasa.

NNPP ta magantu kan dakatar da Kwankwaso

Mun ba ku labarin cewa NNPP reshen jihar Kano ta yi fatali da dakatarwar da wani tsaginta ya yiwa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Jam'iyyar ta kuma yi fatali da korar da aka yiwa jagoranta na ƙasa kuma ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Hashim Dungurawa, ya bayyana matakin dakatarwar da korar a matsayin haramtacce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.