Ministan Tinubu Ya Gana da Ƴan Majalisar Amintattun PDP a Abuja, Bayanai Sun Fito

Ministan Tinubu Ya Gana da Ƴan Majalisar Amintattun PDP a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya gana da ƴan majalisar amintattu na PDP (BoT) a daren ranar Talata, 17 ga watan Satumba 2024
  • Legit Hausa ta fahimci cewa wannan taro wani wani ɓangare ne a yunƙurin BoT na kawo ƙarshen rigimar siyasar da ta dabaibaye jihar Ribas
  • Daga canjin gwamnati a Mayun 2023, Wike da magabacinsa, Siminalayi Fubara suka raba gari kan wanda zai zama jagoran PDP a jihar Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gana da majalisar amintattu (BoT) na PDP karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara a daren Talata.

A watan Agusta, BoT ta rubutawa Nyesom Wike wasiƙa, inda suka nemi zama da shi don warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP musamman a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamnonin PDP sun fara ƙokarin sauya shugaban jam'iyya na ƙasa

Nyesom Wike.
Wike ya gana da ƴan majalisar amintattun PDP a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Dalilin PDP-BoT na zama da Nyesom Wike

Kamar yadda Punch ta ruwaito, majalisar amintattun ta nemi zama da Wike kwanaki ƙalilan bayan ganawa da gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Wike dai ya jima yana takun saƙa da magajinsa, Gwamna Fubara kan jagorancin PDP reshen jihar Ribas.

PDP: Rikicin Wike da gwamna Fubara

Rigimar ta yi ƙamari har sai da ministan Abuja ya fito ya faɗawa duniya cewa ba zai sake marawa Gwamna Fubara baya ba a siyasa.

A baya-bayan nan, gwamnonin PDP suka tsoma baki a danbarwar siyasar jihar Ribas, inda suka ce suna goyon bayan Gwamna Fubara.

Har ila yau an ji gwamnonin PDP na cewa Wike ya zama moli mara mafani domin kowa ya yi fatali da shi a jam'iyyar.

Kwamitin NWC ya goyi bayan Wike

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Sai dai a kwanakin baya, mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum ya mikawa Wike jagorancin PDP a jihar Ribas. 

Da wannan mataki na NWC, Wike ya zama jagoran PDP a Ribas saɓanin al'adar jam'iyyun siyasa na ba gwamna ragamar jagoranci a matakin jiha.

Zaman majalisar PDP-BOT da Ministan

Ganin yadda abubuwa ke ta taɓarɓarewa a siyasar Ribas, ƴan kwamitin BoT suka nemi zama da Wike domin lalubo hanyar masalaha da warware rigimarsa da Fubara.

Rahotan Vanaguard ya nuna cewa Wike ya gana da ƴan kwamitin amintattun PDP a sirrance domin ba a bar ƴan jarida sun shiga domin ɗauko rahoto ba.

Gwamnan Bauchi ya maida martani ga Wike

A wani rahoton kuma gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya mayar da martani ga ministan Abuja kan barazanar da ya yi wa gwamnonin PDP.

Sanata Bala ya ce ba wanda zai kunna wuta a Bauchi ya ci nasara saboda akwai wadataccen ruwan da ba zai bar wutar ta ci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262