NNPP ta Samu Koma Baya: Hadimin Abba Ya Ajiye Muƙami, Ya Sauya Sheƙa

NNPP ta Samu Koma Baya: Hadimin Abba Ya Ajiye Muƙami, Ya Sauya Sheƙa

  • Jami'yyar NNPP mai mulki a Kano ta samu koma baya yayin da wasu daga cikin jiga jigan jami'yyar suka sauya sheka
  • Alhaji Sani Dabo ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya
  • Haka zalika wani dan siyasa a karamar hukumar Kabo, Rabi'u Alhassan Durum ya sauya sheka ya koma jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yan siyasa na cigaba da sauya sheka a Kano yayin da ake shirin zaben kananan hukumomi.

Wasu jiga jigan yan jam'iyyar NNPP a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana rade radin tuge shi, Ganduje ya damƙi Sanata daga PDP zuwa APC

Barau Jibrin
Yan NNPP sun sauya sheka zuwa APC a Kano. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauya sheƙa: Hadimin Abba a ajiye muƙami

Wani hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Sani Dambo ya ajiye matsayin mai ba Abba Kabir Yusuf shawara na musamman.

Alhaji Sani Dabo ya tabbatar da ficewa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ajiye muƙamin da ya yi a gwamnatin Abba.

Haka zalika babban ɗan siyasa a karamar hukumar Kabo, Rabi'u Alhassan Durum ya sanar da ficewa daga NNPP zuwa APC.

Sanata Barau Jibrin ya karbi yan NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi yan NNPP din zuwa APC a Abuja.

Barau Jibrin ya ce komawar Sani Dambo zuwa NNPP abu ne mai muhimmanci kuma yana fatan za su yi aiki tare wajen kawo cigaba a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Haka zalika ya ce Sani Dambo da Rabi'u Alhassan Durum sun kasace jajirtattun mutane da za su iya kawo sauyi a Najeriya.

Yan Kannywood sun koma APC a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa a kwanan nan ana kara samun yan jam'iyyar NNPP a jihar Kano na cigaba da suka sauya sheka zuwa jami'yyar APC.

A wannan karon, wasu fitattun jaruman Kannywood sun kara ficewa daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng