Kitimurmurar Atiku da Wike: Shugaban Jam’iyya Ya Fede Biri Har Wutsiya Game da Zunuban Wike a PDP

Kitimurmurar Atiku da Wike: Shugaban Jam’iyya Ya Fede Biri Har Wutsiya Game da Zunuban Wike a PDP

  • Shugaban PDP ya yi tsokaci kan lamarin Wike da korafe-korafen da ake yi a kansa bayan zaben shugaban kasa
  • Tun bayan rasa takarar shugaban kasa Wike ya fara rabar APC har ta kai ya zama minista a gwamnatin Tinubu
  • An bayyana hanyar da za a bi wajen ladabtar da Wike yadda ya dace, amma ba lallai a iya daukar mataki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya yi tsokaci kan buyayyun zarge-zarge da ake yi kan tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kan cin dunduniyar jam’iyya.

Majiya ta nakalto cewa, ana zargin Damagum da goyon bayan Wike a taron gangamin da jam’iyyar PDP ta gudanar.

Damagum ya magantu kan lamarin Wike
Damagum ya yi tsokaci kan batun Wike da PDP | Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, ana zargin Wike da cin dunduniyar jam’iyya a zaben shugaban kasa na 2023, inda ake fargabar ya goyi bayan jam’iyyar APC a zaben tun bayan da rasa tikitin takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"Dino Melaye ya tsaya takarar gwamna, bai kadawa kansa kuri'a ba," inji shugaban PDP

Ban goyi bayan Wike ba, ina da alaka mai kyau da Atiku, Damagum

Sai dai, da yake wanke zargin cewa ya goyi bayan Wike a taron gangamin na PDP, Damagum ya ce bashi da dalilin yin hakan.

A cewarsa, yana da alaka mai karfi tsakaninsa da Atiku da Wike, kuma Wike da kansa ya bayyana bai samu wani taimako daga gare shi ba.

A cewarsa:

“Wike da kansa ya fadi a talabijin – ina ga a hirarsa ta karshe kenan. cewa ban taimaka masa ba a taron gangami.
“Ya nemi taimako na, amma ban taimaka masa ba. Don haka, tun da da kansa ya amince ya fadi, wani taimako zai nema daga wuri na yanzu da na gaza masa a baya.”

Batun hukunta Wike kan cin dunduniyar jam’iyya

Kara karanta wannan

"Da mu muke mulki, ba za a janye tallafin fetur kamar yadda Tinubu ya yi ba," inji shugaban PDP

A bangare guda, Damagum ya yi tsokaci kan batun daukar mataki kan Wike bisa yiwa PDP zagon kasa da kuma rabar inuwar APC.

A cewar Damagum, ba huruminsa bane ya nuna yatsa tare da daukar mataki kai tsaye, aiki ne na matakin jihar da Wike ya fito.

A cewarsa:

“Wike mamba ne daga jihar Rivers, kuma inda wani korafi ya tashi, daga can zai fito. Gunduma ce za ka kawo korafi zuwa hedkwata daga nan sai mu kai gaban kwamitin ladabtarwa.”

Janye fetur da Tinubu ya yi

A wani labarin, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya bayyana irin kokarin da jam’iyyarsu za ta yi da ita ke kan mulki aka janye tallafin man fetur.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, Damagum ya bayyana cewa, da PDP ke kan mulki, da kuwa tabbas sai an yi tunani mai zurfi kafin janye tallafin man fetur a kasar.

Da yake kwatanta yadda gwamnatin shugaba Tinubu ta bambanta da yadda PDP ta mulki kasar, ya ce a kullum jam’iyyarsu na duba lamarin talaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.