“Dino Melaye Ya Tsaya Takarar Gwamna, Bai Kadawa Kansa Kuri’a Ba,” Inji Shugaban PDP

“Dino Melaye Ya Tsaya Takarar Gwamna, Bai Kadawa Kansa Kuri’a Ba,” Inji Shugaban PDP

  • A wata tattaunawa da aka yi da shugaban PDP na kasa, ya tono lamarin da ya shafi faduwar Dino Melaye a zaben gwamnan Kogi
  • Akwai ‘yar hatsaniya da jam’iyyar PDP ke fuskanta tun bayan kammala zaben shugaban kasa na bara
  • A matsayinta na jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya, PDP na kokarin bayyana yadda za ta ci nasara a zabukan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya tona yadda Dan takarar gwamnan jihar Kogi a zaben da ya gabata, Sanata Dino Melaye ya gaza kadawa kansa kuri’a.

Damagum ya koka da yadda Dino ya maida lamarin takararsa wasa har ta kai ga ya gaza samun nasara a zaben.

Idan baku manta ba, Dino ya yi wasu batutuwa da ke nuna rashin kishin jam’iyya da kuma alamar dawowa daga rakiyarta a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

"Da mu muke mulki, ba za a janye tallafin fetur kamar yadda Tinubu ya yi ba," inji shugaban PDP

Damagum ya bude aiki kan ikrarin Dino Melaye
Martanin PDP kan batutuwan Dino Melaye | Hoto: Peoples Democratic Party
Asali: Twitter

Dino ne matsalar kansa a zaben Kogi, inji Damagum

Da yake bayyana gaskiyar abin da ya faru a zaben Kogi, Damagum ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yana daya daga cikin matsalolin. Me yasa? Saboda ya tsaya takarar gwamnan Kogi amma bai ma kadawa kansa kuri’a ba. Ka fada a ko’ina: bai ma halarci wurin kada kuri’a ba.”

Ya kara da cewa:

“A matsayinsa na dan takara. Don haka, zan barka ka yi hukunci duba da wannan.Waye da gaske mai lalata jam’iyya?

Me ya kamata Dino ya yi a zaben Kogi?

Damagum ya yi amanna da cewa, ya rataya a wuyan duk wani dan takara ya yi hobbasa wajen tabbatar da ya samu nasara a zabe.

Hakazalika, ya ce ana iya faduwa, amma kada ya zama dan takara bai nuna wani kokarin cin zabe ba.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

Ya ce:

“Idan jam’iyya na da kara ta ba ka dama a cikinta ka yi takara, ya rataya a wuyanka ka habaka sa’arta. Tabbas, za ka iya takara ka yi nasara ko ka fadi, amma dai ka fadi da nauyi idan ya zama dole.”

Za mu ci zabe a Edo, inji Damagum

A bangare guda, Damagum, ya yi magana kan zaben gwamnan Edo, inda ya bayyana kwarin gwiwa game da zaben da za a yi.

Umar Damagum ya bayyana cewa 'ya'yan jam’iyyar za su yi amfani da jininsu wajen kare kuri’unsu a zaben gwamnan da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Shugaban na PDP ya kuma gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan sanar da sakamakon zaben cikin tsakar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.