“Da Mu Muke Mulki, Ba Za a Janye Tallafin Fetur Kamar Yadda Tinubu Ya Yi Ba,” Inji Shugaban PDP

“Da Mu Muke Mulki, Ba Za a Janye Tallafin Fetur Kamar Yadda Tinubu Ya Yi Ba,” Inji Shugaban PDP

  • Shugaban jam’iyyar PDP ya bayyana cewa, akwai ganganci wajen janye tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi baktatan
  • Damagum ya ce ba zai yiwu dan takarar PDP na shugaban kasa ya janye tallafi haka siddan ba tare da duba ga wasu lamurra ba
  • Ya yi waiwaye ga yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara farashin mai da kuma samar da mafita mai sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum ya bayyana irin kokarin da jam’iyyarsu za ta yi da ita ke kan mulki aka janye tallafin man fetur.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, Damagum ya bayyana cewa, da PDP ke kan mulki, da kuwa tabbas sai an yi tunani mai zurfi kafin janye tallafin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

Aikin dana-sani: Matashi ya shiga hannu bayan yin ajalin danginsa na kusa

Idan baku manta ba, janye tallafin man fetur ya jawo wahalhalu ga ‘yan Najeriya, inda ake sayar da litar mai a farashin da yah aura N1000 a kasar.

Shugaban PDP kan batun janye tallafin mai
PDP ba za ta tsoma 'yan Najeriya a yanayin da ake ciki ba, Damagum | Hoto: Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Cire tallafin mai a zamanin Goodluck Jonathan

Da yake kwatanta yadda gwamnatin shugaba Tinubu ta bambanta da yadda PDP ta mulki kasar, ya ce a kullum jam’iyyarsu na duba lamarin talaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayyana cewa:

“Na tuna lokacin da Jonathan ya kara farashin mai, an tada jijiyar wuta. Ya yi martani ne ta hanyar rage farashin tare da samar da zabin da zai saukakawa al’umma wahalhwalu.
“Gwamnati lamari ne na yiwa al’umma hidima, ba aiki ne na kashin-kai da kuma ahali ba.”

Atiku ya ce zai cire tallafin man fetur

Da yake tsaftace aniyar dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar kan kudurin janye tallafin mai, Damagum ya ce Atiku ba zai yi irin na Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

A cewarsa, yana da yakinin Atiku ba zai sanar da janye tallafin ba a lokacin rantsar dashi kamar yadda Tinubu ya yi ba.

A kalamansa, cewa ya yi:

“Tabbas (zai cire tallafi), amma baktatan bayan rantsar dashi ba, ba tare da fahimtar ya lamurra suke ba.”

Za mu ci zabe a Edo, inji Damagum

A bangare guda, Damagum, ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo, inda ya bayyana kwarin gwiwa game da zaben da za a yi.

Umar Damagum ya bayyana cewa 'ya'yan jam’iyyar za su yi amfani da jininsu wajen kare kuri’unsu a zaben gwamnan da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Shugaban na PDP ya kuma gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan sanar da sakamakon zaben cikin tsakar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.