PDP Na Neman Birkicewa yayin da Wike Ya Sake Kalubalantar Gwamnonin Jam'iyyar
- Nyesom Ezenwo Wike ya saƙe fitowa ya ƙalubalanci gwamnonin jam'iyyar PDP waɗanda baya ga maciji da su
- Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya ƙalubalance su kan cewa babu wanda ya isa ya ce ya ci amanar jam'iyyar PDP
- Wike ya gaya musu cewa idan har suna jin sun isa, to su fito fili ƙarara a gidan talabijin su gayawa duniya cewa shi maci amana ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake ƙalubalantar gwamnonin PDP.
Wike ya ƙalubalanci duk wani gwamna ko wani shugaba a jam’iyyar PDP, da ya fito fili ƙarara ya kira shi da maci amana.
Nyesom Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirin su na 'Politics Today'.
Jaridar Vanguard wacce ta bibiyi tattaunawar ta ce Wike ya ce idan akwai wanda ya isa to ya fito ya zarge shi da zama maci amana.
Wike ya nuna yatsa ga gwamnonin PDP
"Kafin na karɓi muƙamin minista, na rubuta takarda zuwa ga PDP a jihata, na rubuta takarda zuwa ga PDP a shiyya ta, na rubuta takarda zuwa ga PDP ta ƙasa, wanene ya isa a PDP ya ce ni maci amana ne."
"Ina ƙalubalantar duk wanda ya isa a PDP, duk wani gwamna da ya isa, duk wani mamba na NWC da ya isa, da ya fito a gidan talabijin ya ce ni maci amana ne."
"A 2023 ba na ce ba zan marawa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP baya ba saboda hakan ya saɓawa gaskiya da adalci? Shin munafurce na yi hakan?
"Shin PDP ba ta ci zaɓen gwamna ba? shin ba ta ci zaɓen ƴan majalisun tarayya ba? shin ba ta ci zaɓen ƴan majalisar jiha ba? Ina ƙalubalantar dukkanin waɗannan gwamnonin idan akwai wanda PDP ta lashe kaso 100% kamar yadda muka yi."
- Nyesom Wike
Wike ya yi nasara kan gwamnonin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP ta ƙasa ya amince da gangamin taron zaɓen shugabannin jam'iyyar da aka yi a jihar Ribas.
Wannan dai wata alama ce da ke nuna shugabannin PDP na ƙasa na goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike a rikicin Ribas domin magoya bayansa ne suka yi nasara.
Asali: Legit.ng