"Ba Zan Sake Mara Maka Baya a Siyasa ba": Ministan Tinubu ga Yaronsa Gwamnan PDP

"Ba Zan Sake Mara Maka Baya a Siyasa ba": Ministan Tinubu ga Yaronsa Gwamnan PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya caccaki Gwamna Siminalayi Fubara kan karairayi da yake yi masa
  • Wike ya koka kan yadda ya sadaukar da wahalar da wasu suka sha domin tabbatar da Fubara ya zama gwamnan jihar
  • Ministan ya ce har karshen rayuwarsa ba zai sake goyon bayan Fubara ba a siyasa saboda butulci da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fusata kan rigimar da ake yi a jihar Rivers.

Wike ya ce har karshen rayuwarsa ba zai sake goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara ba a siyasa.

Ministan Tinubu ya caccaki gwamnan PDP kan yi masa karairayi
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya soki Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Wike ya caccaki Fubara kan siyasar Rivers

Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

Mawakin Musulunci ya fadi dalilin yin murabus daga matsayin hadimin gwamna

Wike ya caccaki Gwamna Fubara inda ya ke zarginsa da yi masa karairayi da dama a rayuwarsa.

Ya koka kan yadda wasu da suka bautu a siyasa amma ya tsallake su domin goyawa Fubara baya a siyasa.

Wike ya fadi yadda ya sadaukar da komai

"Ba zan sake goyon bayan Fubara a siyasance ba a rayuwa ta, kowa ya sani ba maganar ni ake yi ba, mutane da yawa sun sha wahala."
"Mutane da yawa sun bautu, ko mataki na 50 ba ka ciki amma na yi magana da yan Ogoni da saura cewa ya kamata mu yi kaza."
"Ka zo ka juya magana cewa ina neman N50,000 ko N100,000 kana ta karya, ni da daura ka kuma na dawo roko."

Nyesom Wike

Wike ya caccaki gwamnonin PDP a Najeriya

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur ya tilastawa Gwamna karawa ma'aikata hutu a kowane mako

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya yi barazana ga jam'iyyar PDP idan har suka fusata shi ya fice daga cikinta.

Wike ya ce da zarar ya fusata har ya gudu daga PDP to tabbas karshenta ya zo kuma dubban yan jam'iyyar za su fita.

Ministan harkokin birnin Abuja ya bayyana haka ne a sakatariyar jam'iyyar da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers a makon jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.