An Zargi Gwamna a Arewa da Fatali da Umarnin Tinubu, APC Ta Fusata

An Zargi Gwamna a Arewa da Fatali da Umarnin Tinubu, APC Ta Fusata

  • Jam'iyyar APC ta caccaki Gwamna Alia Hyacinth na Benue kan rikicin siyasar cikin gidan a jihar da ke faruwa
  • Mambobin APC a Majalisar Tarayya su suka zargi gwamnan da neman ruguza jam'iyyar domin biyan buƙatar kansa
  • Wannan na zuwa ne bayan kin mutunta gayyatar da aka yi wa gwamnan domin sasantawa wanda Bola Tinubu ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Mambobin APC a Majalisar Tarayya sun zargi gwamnan Benue da yi wa jam'iyyar zagon kasa.

Mambobin suna zargin Gwamna Alia Hyacinth da rashin mutunta gayyatar Shugaba Bola Tinubu.

APC ta soki gwamna a Arewa da mata zagon kasa
Gwamna Alia Hyacinth ya shiga matsala bayan zargin zagon kasa ga APC. Hoto: Alia Hyacinth.
Asali: Twitter

An zargi Gwamna Alia da kin mutunta Tinubu

Kakakin kungiyar, Philip Agbese shi ya bayyana haka a cikin wata wasika a yau Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Ya ci mutuncin jam'iyya': PDP ta dakatar da tsohon dan takarar gwamna a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Agbese ya zargi gwamnan da raina umarnin Tinubu bayan gayyatarsa sulhu kan rikicin da ke gudana a jam'iyyar.

Ya zargi gwamnan da neman ruguza jam'iyyar musamman a Benue saboda biyan bukatunsa, The Guardian ta ruwaito.

Har ila yau, Agbese ya ce yanzu a bayyane yake, matsalar APC a jihar Benue ba kowa ba ne illa Gwamna Alia Hyacinth.

Mambobin jam'iyyar sun zargi Alia da hada kai da wadanda ba yan APC ba domin yakar Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Jam'iyyar APC ta zargi Gwamna da yakar Akume

"Bayan yin nasara a zaben jihar Benue, wasu shaidanu da suka yi kokarin hana shi nasara, sun fito masa a mafarki tare da tsoratar da shi."
"Abin takaici yanzu ya haɗa baki da su domin cigaba da yakar George Akume."

- Philip Agbese

Kara karanta wannan

"Mun damu da halin da a ke ciki": Shugabannin APC sun shirya ganawa da Tinubu

Sai dai Agbese ya tabbatar da cewa yana da kwarin guiwa rikicin zai zo karshe duba da yadda Tinubu ya himmatu wurin dinke barakar.

Gwamna Alia ya rufe kamfanin Ortom

Kun ji cewa gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom kan zargin kin biyan haraji na makudan kudi.

Ana zargin kamfanin mai suna Oracle Business mallakin tsohon gwamna, Ortom da kin biyan haraji har N93.5m.

Sai dai wasu na ganin hakan bita da kullin siyasa ne da ake yi domin kassara harkokin kasuwancin Ortom a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.