Kudin Takara: Bayan Umarnin Kotu, KANSIEC Ta Sassauto daga Karbar N10m, N5m a Kano

Kudin Takara: Bayan Umarnin Kotu, KANSIEC Ta Sassauto daga Karbar N10m, N5m a Kano

  • Kotu a Kano ta tilasta wa hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha (KANSIEC) rage kudin fom na takarar kananan hukumomi
  • A baya, hukumar KANSIEC ta sanya Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fom din tsaya wa takara ga shugabannin kananan hukumomi
  • Su kuma kansiloli za su sayi fom din a kan Naira Miliyan biyar a zaben da za a gudanar a watan Oktoban 2024 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), ta rage kudin fom din tsaya wa takara a zaben kananan hukumomin jihar dake tafe.

Kara karanta wannan

Badakalar N440m: ICPC ta dura kan kakakin majalisar Kano da wasu mutane 4

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki dangane da zaben ƙananan hukumomin jihar da za a yi a watan Oktoba.

Kano map
KANSIEC ta rage kudin fom din takara a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Farfesa Malumfashi ya ce an yi ragin ne biyo bayan umarnin kotu na a sake waiwayar kudin sayen fom domin tsaya wa takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa ne kudin fom a zaben kananan hukumomi?

Voice of Nigeria ta tattaro cewa a yanzu, hukumar KANSIEC ta amince mai neman kujerar shugaban karamar hukuma ya biya Naira Miliyan tara.

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ya bayyana cewa masu neman kujerun kansiloli za su sayi fom dinsu a kan Naira Miliyan hudu.

Wannan na nufin hukumar zaben ta amince da rage Naira Miliyan guda, lamarin da Farfesa Malumfashi ya ce an mutunta umarnin kotu.

Kara karanta wannan

NNPP ta fito da mace a matsayin 'yar takarar shugaban karamar hukumar Kano

KANSIEC ta yabi jam'iyyu kan shiga zaben Kano

Malumfashi ya bayyana jin dadi da yadda sauran jam'iyyun siyasa, musamman APC ta amince da shiga zaben kananan hukumomin jihar.

Ya ce hakan na nuni da amince wa da nagartar hukumar, tare da daukar alkawarin cewa KANSIEC za ta gudanar da zabukan da adalci.

Zaben Kano: KANSIEC ta tsayar da kudin fom

A baya kun samu labari hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC), ta yanke kudin sayen fom domin tsaya wa takara a zaben kananan hukumomi.

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ya bayyana cewa an amince da karbar Naira Miliyan 10 a matsayin na sayen fom na shugaban karamar hukuma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.