Gwamnonin PDP Sun Yi Rashin Nasara a Rikicinsu da Ministan Shugaba Tinubu

Gwamnonin PDP Sun Yi Rashin Nasara a Rikicinsu da Ministan Shugaba Tinubu

  • Kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) ya amince da zaɓen shugabannin da aka yi a jihar Ribas, wanda magoya bayan Wike suka yi nasara
  • Wannan na nufin gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi rashin nasara a yaƙin da suka fara da ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Tun farko dai rikicin Wike da Simi Fubara ya dawo ɗanye kan shugabancin PDP a Ribas, wanda gwamnoni suka marawa Fubara baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP ta ƙasa ya amince da gangamin taron zaɓen shugabannin jam'iyyar da aka yi a jihar Ribas.

Wannan dai wata alama ce da ke nuna shugabannin PDP na ƙasa na goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike a rikicin Ribas domin magoya bayansa ne suka yi nasara.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Gwamnonin PDP da Wike.
NWC ya goyi bayan nasarar Wike a zaɓukan shugabannin PDP a jihar Ribas Hoto: @SenBalaMohammed, @GovWike
Asali: Twitter

A rahoton Punch, wasu majiyoyi sun ce NWC karƙashin shugaban PDP, Umar Damagum ya ɗauki wannan matakin ne a wani taro da ya gudana a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An daga taron PDP NEC?

A taron wanda ya gudana ranar Alhamis a hedkwatar PDP, NWC ya kuma amince da ɗaga taron majalisar zartaswa (NEC) daga 26 ga Satumba zuwa 24 ga Oktoba, 2024.

Ɗage taron NEC da anincewa da zaɓaɓɓun shugabannin zai ba tsagin Wike damar karɓe ragamar jam'iyyar PDP a jihar Ribas, in ji majiyoyin.

Meyasa gwamnonin PDP ke faɗa da Wike?

Idan ba ku manta ba PDP ta jima tana fama da rigingimun cikin gida, a baya bayan nan, aka fara takun saƙa tsakanin gwamnonin jam'iyyar da ministan Abuja.

Rigimar ta fara ne lokacin da gwamnonin PDP suka fito suka nuna goyon baya ga Fubara, hakan ya fusata Wike har ya yi barazanar kunno masu wuta jihohinsu.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Gwamna Obaseki ya fallasa makarkashiyar da ake yiwa PDP

PDP - NWC ya ba tsagin Wike cikakkiyar dama

Wani babban kusa a NWC ya tabbatar da cewa sun amince da gangamin da aka yi a Ribas kuma an ɗaga taron NEC.

A cewarsa, tsagin Wike ya cimma burinsa domin babu wanda ya isa ya soke matakin da NWC ta ɗauka face NEC, kuma an ɗage taron zuwa watan Oktoba.

PDP ta dakatar da Dino Melaye

A wani rahoton kuma jam'iyyar hamayya ta PDP a Kogi ta dakatar da tsohon dan takarar gwamnanta na zaben 2023 a jihar, Dino Melaye.

An ruwaito cewa PDP ta dakatar da Sanata Melaye ne bisa zargin ya aikata laifuffukan da suka saba da'a da cin mutuncin jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262