Kano: APC Ta Bugi Kirji kan Zaben Kananan Hukumomi, Ta Fadi Shirin da Ta Yi
- Shugaban jam'iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana shirin jam'iyyar game da zaben kananan hukumomi da za a yi
- Abbas ya ce APC ta shirya shiga zaben kananan hukumomin Kano 44 da za a yi a ranar 24 watan Oktobar 2024 domin a dama da ita
- Ya ce APC ta fara shiri wurin wayar da kan mambobinta domin shiga zaben, za a fara da yin zabukan fidda gwani na cikin jam'iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar APC a jihar Kano ta yi magana kan zaben kananan hukumomi da za a yi.
Jam'iyyar ta ce a shirye ta ke a zaben da za a yi a jihar inda ta ce tana sa ran samun nasara a zaben ranar 24 ga watan Oktobar 2024.
Kano: APC ta shiryawa zaben kananan hukumomi
Shugaban jam'iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Alhamis 12 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.
Abbas ya ce yanzu haka sun shirya za su gudanar da zabukan fidda gwani a jihar domin fitar da yan takara.
Ya ce APC ta fara hada kan yan jam'iyyar tare da wayar da kansu domin fita zaben da za a gudanar, Daily Post ta ruwaito.
Jam'iyyar APC ta roki hukumar zaben jihar Kano
"Mu na yin duk mai yiyuwa domin ganin dubban magoya bayanmu sun shiga an dama da su a zaben kananan hukumomi."
"Mu na kira ga hukumar zaben jihar Kano da ta ba kowa dama domin gudanar da zaben cikin lumana da adalci."
- Abdullahi Abbas
A ranar 26 Oktoba ne hukumar zaben mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar.
Mace za ta zama 'yar takara a Kano
Kun ji cewa jam'iyya mai mulki a Kano ta fitar da yan takara akalla 484 a zaben kananan hukumomi da za a gudanar nan gaba kadan.
Daga cikin masu neman mukamai daban-daban, NNPP ta tsayar da mace guda daya, Sa'adatu Salisu a takarar shugabar karamar hukuma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng