Zaben 2027: Malamin Addini Ya Ba Kwankwaso Shawara kan Karawa da Tinubu

Zaben 2027: Malamin Addini Ya Ba Kwankwaso Shawara kan Karawa da Tinubu

  • Primate Babatunde Elijah Ayodele ya shawarci Rabiu Musa Kwankwaso, da ya haƙura da burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa
  • A zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, Kwankwaso ya zo a matsayi na huɗu inda ya samu ƙuri’u kusan miliyan ɗaya da rabi
  • Kwankwaso ya samu mafi yawan ƙuri’unsa ne daga jiharsa ta Kano da ke yankin Arewa maso Yamma inda yake da ɗimbin magoya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya ba Rabiu Musa Kwankwaso shawara.

Primate Ayodele ya buƙaci Rabi’u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, da ka da ya sake tsayawa takara a nan gaba.

Kara karanta wannan

NAF: Jirgin sojoji ya yi luguden wuta kan ƴan bindiga, ya hallaka da dama a Arewa

Fasto Ayodele ya ba Kwankwaso shawara
Primate Ayodele ya bukaci Kwankwaso ya hakura da takara Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Fasto Ayodele ya ba Kwankwaso shawara

Babban faston ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na X ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saƙon na Primate Ayodele na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan siyasar Najeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

A yayin da Kwankwaso yake shirin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa, Primate Ayodele ya shawarci tsohon gwamnan na Kano da ka da ya ɓarnatar da dukiyarsa.

“Kwankwaso, ka manta da takarar shugaban ƙasa. Ba na ganin cewa za ka yi nasara. Ba na ganin cewa za ka lashe zaɓen shugaban ƙasa. Ka da ka ɓarnatar da dukiyarka."

- Primate Babatunde Elijah Ayodele

Karanta wasu labaran kan Kwankwaso

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban APC ya yi hasashen makomar Shugaba Tinubu a 2027

Jam'iyyar PDP ta caccaki Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta yi kakkausar suka ga jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso bisa iƙirarin da ya yi na cewa PDP ta mutu.

Sakataren yaɗa labarai na PDP, Debo Ologunagba ya bayyana Kwankwaso a matsayin “ɗan siyasar da bai da wani tasiri” wanda yake faɗi tashin tafiyar da jam’iyyar da ke da iko a jiha ɗaya kacal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng