Dan Majalisar Tarayya a Arewa Ya Shiga Matsala, Mazabarsa na Shirin Masa Kiranye
- Dan Majalisar Tarayya a jihar Yobe, Hon. Lawan Shettima Ali yana fuskantar matsala bayan shirin yi masa kiranye
- Yan mazabar Ngazargamu da ke jihar Yobe sun nuna damuwa kan yadda dan Majalisar ya yi fatali da su a yankin
- Wasu jagororin da ke mazabar Geidam da Yunusari da Bursari sun fadi shirinsu na yin kiranye ga dan Majalisar nasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Yobe - Wasu mazauna mazabar Ngazargamu daga jihar Yobe sun fusata da dan Majalisarsu da ke Tarayya.
Hon. Lawan Shettima Ali yana fuskantar barzanar bayan yan mazabar sun tabbatar da cewa bai tabuka musu komai ba.
'Dan Majalisa na fuskantar barazana a Yobe
Jagororin mazabar da suka hada da Geidam da Yunusari da Bursari sun tabbatar da hakan ga jaridar Aminiya.
Suna zargin dan Majalisar da yin fatali da su tare da wucewa birnin Abuja inda ya mance da su gaba daya.
Wani daga cikin jagororin, Babagana Aisami Geidam ya sanar da yan yankin cewa suna shirin yi wa dan majalisarsu kiranye saboda rashin jagorranci nagari.
Aisami ya kuma zargi dan Majalisar da rashin gabatar da wani kudiri kan matsalolin yankin da suke fama da shi.
Musabbabin shirin yin kiranye ga dan majalisa
"Tafiya ta yi nisa wajen wannan shiri, muna aiki tuƙuru ba dare ba rana domin tabbatar da wannan aikin don samarwa al’umma mafita.”
"Yankin na Ngazargamu ya sha fama da matsalolin tsaro, wanda ya haifar da koma baya ta fuskar ilimi da tattalin arziƙi da noma da sauran fannonin rayuwa."
.- Babagana Aisami
Aisami ya ce amma duk da wadannan tarin matsalolin, dan Majalisar ya kasa kawo sauyi a rayuwar al'umma.
Sarkin Potiskum ya ziyarci Sanusi II
Kun ji cewa Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Umar Bauya ya kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Basaraken ya ce ya zo fadar Sanusi II ne domin yin mubaya'a da nuna goyon baya a gare shi da mutanensa baki daya.
Sarkin ya roki Sanusi II da ya ba da gudunmawarsa wurin karasa gina masallacin Juma'a da suka faro shekarun baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng