APC Ta Yi Martani ga Kwankwaso, Ta Fadi Dalilin Hana Abba Rabon Shinkafar Tinubu

APC Ta Yi Martani ga Kwankwaso, Ta Fadi Dalilin Hana Abba Rabon Shinkafar Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta caccaki Rabi'u Musa Kwankwaso kan kalaman da ya yi na hana gwamna Abba Kabir Yusuf rabon shinkafar Bola Tinubu
  • Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce shugaban kasa Tinubu ya ki ba gwamna Abba ragamar rabon tallafi
  • Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da nuna wariya da bambancin siyasa, lamarin da APC ta ce tsabar rashawa ce ta jawo haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - APC ta yi martani kan kalaman jagoran NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso na zargin gwamnatin tarayya da nuna wariya ga gwamna Abba Kabir Yusuf.

Shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas ya bukaci Sanata Kwankwaso ya tuntubi gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan tallafin da aka bayar a baya saboda talakawa.

Kara karanta wannan

"Zaluncin gwamnatin Tinubu ya fi na soja:" Atiku ya soki yadda ake murkushe kungiyoyi

Kwankwaso
APC ta yi martani kan kalaman Sanata Kwankwaso Hoto: Aliyu Abubakar Aliyu/Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Abdullahi Abbas ya ce gwamnatin tarayya na kokari wajen bullo da hanyoyin rage radadin da talakawa ke ciki, amma gwamnatin Kano na kawo cikas.

APC ta zargi gwamnatin Abba da almundahana

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da almundahanar tallafin gwamnatin tarayya.

Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatin Tinubu ta daina mika tallafin da ya kamata a raba ga talakawan Kano saboda gudun kar wasu mukarraban gwamnati su cinye.

"Akwai rashawa a gwamnatin Abba," APC

Jam'iyyar APC a Kano ta yi zargin wasu manyan jami'an gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano da rashawa da karkatar da tallafin talakawa.

Shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas ne ya bayyana haka, inda ya ce wannan dalilin ne ya sa tallafin gwamnatin Tinubu ba ta karasa wa ga talaka.

Kara karanta wannan

Shinkafar Tinubu: Kwankwaso ya zargi gwamnati da ware Abba cikin gwamnoni 36

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin APC

A baya kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya koka kan yadda gwamnatin tarayya ke nuna wariya ga gwamnan Kano.

Sanata Kwankwaso ya ce ana ware gwamna Abba Kabir Yusuf daga raba tallafin gwamnatin tarayya da ake ba gwamnoni, sannan ana yawan sauya shugabannin DSS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.