Ana Shirin Zabe, Hadiman Gwamna 4 Sun Watsa Masa Kasa a Ido, Sun Bar PDP

Ana Shirin Zabe, Hadiman Gwamna 4 Sun Watsa Masa Kasa a Ido, Sun Bar PDP

  • Gwamnan jihar Edo ya yi babban rashi bayan hadimansa guda hudu sun yi murabus ana daf da gudanar da zabe
  • Hadiman guda hudu sun ajiye aikin ne da ficewa daga PDP saboda rashin biyansu albashi tun farkon nada su
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Edo nan da kwanaki 11 kacal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Kwanaki 11 kafin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, jam'iyyar PDP ta gamu da cikas.

Hadiman Gwamna Godwin Obaseki guda hudu sun yi murabus daga mukamansu tare da ficewa daga PDP.

Hadiman gwamnan PDP 4 sun yi murabus ana shirin zabe
Hadiman Gwamna Godwin Obaseki 4 sun yi murabus a jihar Edo. Hoto: Godwin Obaseki.
Asali: Twitter

Edo: Hadiman Gwamna Obaseki 4 sun yi murabus

Kara karanta wannan

An samu asarar rai bayan gini ya sake rikitowa a Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar bayan turawa shugaban jam'iyyar a karamar hukumarsu, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda suka yi murabus din akwai Osayande Emenya daga karamar hukumar Oredo da Henry Osaheni shi ma daga karamar hukumar.

Sai kuma Efosa Edo-Osagie daga karamar hukumar Oredo da kuma Timothy Edokpolor daga karamar hukumar Ikpoba Okha.

Musabbabin murabus din hadiman Obaseki a Edo

Wadanda suka yi murabus din sun bayyana cewa ba a taba biyansu albashi ba tun da aka nada su mukamin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Sun kuma koka kan yadda aka mayar da asalin asalin yan jam'iyyar saniyar ware wurin gudanar da lamuranta.

Har ila yau, tsofaffin hadiman ba su bayyana shirinsu na gaba ba kan komar siyasarsu a jihar ba bayan watsar da jam'iyyar PDP ana shirin yin zabe.

Kara karanta wannan

An rasa muhalli da dukiya: Jihohin Arewa da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a 2024

"Dalilin fada na da Oshiomhole" - Gwamna Obaseki

Kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya fadi ainihin abin da ya haɗa shi da Adams Oshiomhole.

Obaseki ya ce kawai domin ya shirya jana'iza ta musamman ga jigon PDP, Cif Tony Anenih shi ne ya batawa Sanata Oshiomhole rai.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kamfen zaben gwamnan jihar da za a yi a watan Satumbar 2024 da muke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.