APC Ta Faɗi Gwamnan da Take Zargin Yana Shirya Gagarumar Zanga Zanga a Najeriya
- APC ta zargi gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da shirya zanga-zanga domin kawo cikas a zaɓen jihar da Najeriya baki ɗaya
- Kwamitin kamfen APC ya ce gwamnan ya haɗa baki da wasu jihohin da PDP ke mulki domin fara zanga-zanga ranar 15 ga watan Satumba
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Edo wanda za a yi a watan da muke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jam'iyyar APC reshen Edo ta zargi Gwamna Godwin Obaseki da shirya gagarumar zanga-zangar da za ta rikita jihar ranar 15 ga watan Satumba, 2024.
Bayan haka, APC ta kuma yi zargin cewa gwamnan ya fara kulle-ƙullen yadda zai haɗa kai da sauran gwamnonin PDP domin kawo hargitsi a Najeriya.
Daraktan yaɗa labarai na kwamitin kamfen APC a Edo, Prince Kassim Afegbua, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Benin, Vanguard ta ruwaito.
APC na zargin Obaseki da shriya zanga-zanga
Ya ce Gwamna Obaseki ya zayyana shirinsa ne a wurin wani taro a gidan gwamnatin jihar Edo da ke Benin City ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024.
Afegbua ya yi ikirarin cewa taron ya samu halartar wasu da ake zargin suna da hannu wajen kashe Sufetan ƴan sanda, Akor Onu.
Kakakin kwamitin kamfen APC ya yi zargin cewa mataimakin kwamishinan ƴan sanda na Edo ya haɗa baki da gwamnan, ya ba da wasu masu laifi kariya.
Kazalika ya ce a makon da ya wuce, sojoji suka kama ƴaƴan APC bakwai da ƴan PDP uku, amma abin mamakin aka saki ƴan PDP ba tare da ɓata lokaci ba saboda suna da gata.
'Yadda Obaseki ya haɗa baki da wasu jihohi'
Kassim Afegbua ya kara da cewa Gwamna Obaseki ya zuga jihohin da PDP ke mulki kan su jinkirta komawa makaranta saboda zanga-zangar da za su shirya.
"Obaseki ya zuga jihohin da PDP ke mulki su jinkirta komawa hutun makaranta saboda zanga-zangar adawa da gwammatin Bola Tinubu da yake shiryawa da nufin hargitsa Najeriya."
A ƙarshe Afegbua ya yi kira ga hukumomin tsaro musamman sufetan ƴan sanda na kasa da su ankara, su ɗauki matakin daƙile shirin tayar da tarzoma.
A cewarsa, hakan na da matuƙar muhimmanci duba da yadda zaɓen gwamnan jihar Edo ya matso, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Wasu hadiman gwamnan Edo sun bar PDP
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Edo ya yi babban rashi bayan hadimansa guda hudu sun yi murabus ana daf da gudanar da zabe.
Hadiman guda hudu sun ajiye aikin ne da ficewa daga PDP sabodanrashin biyansu albashi tun farkon nada su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng