Gwamna a Arewa Ya Kori Kwamishina daga Aiki, Ya Rantsar da Wasu Mutum 4
- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kori kwamishinan lafiya, Dr. Adamu Sambo, ya naɗa sababbin kwamishinoni uku
- Sanata Bala ya sanar da haka ne a wurin rantsar da sababbin kwamishinonin da ya naɗa a fadar gwamnatinsa da ke birnin Bauchi
- Sakamakon hukuncin kotun koli da ƴantar da kananan hukumomi, ya ce ba zai sake naɗa kwamishina a ma'aikatar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya sallami Dr. Adamu Sambo daga matsayinsa na kwamishinan harkar lafiya.
Gwamnan ya sanar da haka ne a wurin rantsar da sababbin kwamishinoni uku da ya naɗa a faɗar gwamnatin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas.
Channels tv ta ce Bala Mohammed ya kuma naɗa babban mai bada shawara kan harkokin tsaro wanda shi ma aka rantsar da shi tare da kwamishinonin.
Gwamna ya daina naɗa kwamishinan kananan hukumomi
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai sake naɗa kwamishinan ƙananan hukumomi ba bayan Allah ya yi wa tsohon kwamishinan ma'aikatar rasuwa.
A cewar gwamnan babu buƙatar naɗa sabon kwamishinan ƙananan hukumomi tun da kotun ƙoli ta ba su damar cin gashin kansu.
An rasa kwamishinoni a jihar Bauchi
Idan za ku iya tunawa tsohon kwamishinan kananan hukumomin jihar Bauchi, Ahmed Jalam, ya rasu ne a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi a shekarar nan 2024.
Bugu da kari, wasu kwamishinonin biyu sun yi murabus don neman shugabancin kananan hukumomi, sannan gwamnan ya kori babban mai ba shi shawara kan tsaro.
Meyasa gwamna ya kori kwamishinan lafiya?
Da yake jawabi a wurin rantsar da sababbin kwamishinonin, Gwamna Bala ya ce:
"Za mu cike giɓin kwamishinoni uku da suka yi murabus domin tabbatar da kowace karamar hukuma ta samu wakili a majalisar zartaswa. Sannan mun sallami tsohon kwamishinan lafiya.
"Ba zamu sake naɗa kwamishinan kananan hukumomi ba domin rage kashe-kashen kuɗi da kuma bin umarnin kotun ƙoli na ƴantar da ƙananan hukumomi.
"Mun sauke kwamishinan lafiya ba saboda sakaci ba, amma za mu nema masa wani gurbi da ya dace da shi a gwamnati."
Gwamnan Bauchi ya naɗa mutum 4
Gwamna Mohammed ya bayyana Dr. Sani Dambam a matsayin sabon kwamishinan lafiya, wanda ya maye gurbin Dr. Sambo, rahoton The Nation.
Zainab Babbatanka ta zama kwamishiniyar harkokin mata, Mohammed Abdulkadir zai riƙe ma’aikatar kasuwanci, sai kuma Dr. Ahmed Abdurrahman a matsayin mai bada shawa kan tsaro.
Gwamna Bala ya ɗora laifi kan Tinubu
A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ɗora laifin halin ƙuncin rayuwar da ake ciki kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Sanata Bala ya ce tsare-taren tattalin arziƙi na gwamnatin APC ne iya kawo ƙunci, yunwa da wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng