Duk da Suna Adawa, Gwamnan Sokoto Ya Ba PDP Shawara kan Zaben Ciyamomin Jihar

Duk da Suna Adawa, Gwamnan Sokoto Ya Ba PDP Shawara kan Zaben Ciyamomin Jihar

  • Gwamnan jihar Sokoto ya ba da tabbacin cewa za a gudanar da sahihin zaɓe a zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya buƙaci jam'iyyar PDP da ta sake duba matakin da ta ɗauka na ƙauracewa shiga zaɓen
  • Ya bayyana cewa hukumar zaɓen jihar ta ba shi tabbacin cewa duk wanda ya lashe zaɓen za a ba shi nasararsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya yi magana kan zaɓen ƙananan hukumomin da ke gabatowa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatarwa al’ummar jihar ƙudirin gwamnatinsa na gudanar da sahihin zaɓe mai cike gaskiya da adalci a dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Kara karanta wannan

Malami ya gayawa Tinubu kuskuren da yake yi kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya

Gwamnan Sokoto ya magantu kan zaben ciyamomi
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce za a yi sahihin zabe a Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Gwamnan Sokoto ya ba PDP shawara

Gwamnaa ya kuma buƙaci jam’iyyar PDP da ta sake duba matakin da ta ɗauka na ƙauracewa shiga zaɓen ƙananan hukumomin wanda za a yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ahmed ya yi wannan roƙo ne a ranar Lahadi yayin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi takwas na shiyyar Sokoto ta Gabas.

Magoya bayan na APC sun hallara ne a Goronyo domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC gabanin zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Gwamnatin PDP da ta gabata ce ta naɗa shugabannin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Sokoto, kuma ban canza wannan tsarin ba."
"Ina mamakin dalilin da yasa PDP ke tsoron shiga zaɓen da hukumar SIEC ta shirya."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bugi kirji kan zaben 2027, ya fadi abin da zai faru

- Ahmed Aliyu Sokoto

"Za a yi sahihin zaɓe", Gwamna Ahmed

Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatarwa ƴan adawa a jihar cewa a ƙarƙashin gwamnatinsa, hukumar SIEC za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na gaskiya da adalci.

"Na gana shugaban SIEC, kuma ya ba ni tabbacin gudanar da zaɓukan cikin gaskiya. Duk wanda ya lashe zaɓe za a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara."

- Ahmed Aliyu Sokoto

Gwamnan Sokoto ya gargaɗi ƴan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya gargaɗi mutane ko ƙungiyoyi da su daina siyasantar da matsalar tsaro.

Gargaɗin na gwamnan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro a jihar ke ƙara taɓarɓarewa sakamakon ayyukan ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng