Jam'iyyar PDP Ta Fusata kan Kalaman Kwankwaso, Ta Yi Martani Mai Zafi

Jam'iyyar PDP Ta Fusata kan Kalaman Kwankwaso, Ta Yi Martani Mai Zafi

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi martani kan kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa ta mutu murus
  • PDP ta yi watsi da kalaman na jagoran NNPP na ƙasa wanda ta bayyana a matsayin ɗan siyasa wanda baya da tasiri
  • Jam'iyyar ta kuma soki Kwankwaso kan yadda ya mayar da hankalinsa wajen yin takarar shugaban ƙasa yayin da ake cikin halin ƙunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi kakkausar suka ga jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso bisa iƙirarin da ya yi na cewa PDP ta mutu.

Kwankwaso ya yi wannan iƙirarin ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi wajen ƙaddamar da ofishin NNPP a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

"Har da kai a ciki": APC ta caccaki tsohon jigonta kan sukar Buhari da Tinubu

PDP ta caccaki Kwankwaso
Jam'iyyar PDP ta yiwa Kwankwaso wankin babban bargo Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

A martanin da ya mayar, sakataren yaɗa labarai na PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya yi watsi da kalaman na Kwankwaso, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani PDP ta yi wa Kwankwaso?

Debo Ologunagba ya bayyana Kwankwaso a matsayin “ɗan siyasar da baya da wani tasiri” wanda yake faɗi tashin tafiyar da jam’iyyar da ke da iko a jiha ɗaya kacal, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Abin takaici ne cewa ɗan siyasan da ya gaza wanda baya da wani tasiri wanda yake da jiha ɗaya kawai zai yi iƙirarin cewa jam'iyyar da ke da gwamnoni 13, sanatoci masu yawa da tarin ƴan majalisa ta mutu."

- Debo Ologunagba

PDP ta caccaki Kwankwaso

Ya kuma caccaki Kwankwaso kan yadda ya mayar da hankali kan yin takarar shugaban ƙasa yayin da ake cikin halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ya haɗa da hauhawar farashi, karyewar darajar Naira da ƙarin kuɗin fetur.

Kara karanta wannan

Babban alkali ya kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan kwashe watanni a tsare

"Abin takaici ne a wannan lokacin da ake fama da halin ƙunci da wahala, abin da yake zuciyar Sanata Kwankwaso shi ne burinsa na son zama shugaban ƙasa."

- Debo Ologunagba

Olugunagba ya kuma yi nuni da cewa duk wani tasiri a siyasance da Kwankwaso yake iƙirarin ya samu, ya same shi ne lokacin da yake a jam'iyyar PDP.

Kwankwaso ya magantu kan zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Kano jam’iyyar a shirye take ta karɓi ragamar shugabancin ƙasa, jihohi da sauran muƙamai a fadin ƙasar nan zuwa 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng