"Za Mu Kawo Muku Rashin Tsaro ": Ɗan Takarar Gwamna a APC Ya Kwafsa a Bidiyon Kamfe

"Za Mu Kawo Muku Rashin Tsaro ": Ɗan Takarar Gwamna a APC Ya Kwafsa a Bidiyon Kamfe

  • An yi ta cece-kuce bayan kuskuren da dan takarar gwamna APC a jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi yayin kamfe
  • An gudanar da kamfe din ne a karamar hukumar Ovia ta Arewa da ke jihar inda Okpebholo ya tafka kuskure
  • Yayin kamfen, Okpebholo ya yi wa yan jihar alkawarin zai kawo musu 'rashin tsaro' wanda kowa ya sha mamaki a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Dan takarar gwamna a jihar Edo karkashin APC, Monday Okpebholo ya tafka kuskure yayin kamfe.

Okpebholo yayin kamfe a jihar ya yi alkawarin kawo wa al'ummar jihar 'rashin tsaro' idan suka zabe shi.

Kara karanta wannan

2027: Tafiyar Shekarau na kara ƙarfi da Namadi Sambo da Ministan Buhari suka goyi baya

Dan takarar gwamna a APC ya tafka kuskure yayin kamfe
Dan takarar gwamna a APC, Monday Okpebholo ya yi tuntuben harshe a yayin kamfe. Hoto: Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Dan takarar APC ya kwafsa a kamfe

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da jam'iyyar PDP ta wallafa a shafinta na X.

A bidiyon wanda ya karade kafofin sadarwa an gano inda Okpebholo ke cewa zai kawo rashin tsaro a jihar bisa kuskure.

Punch ta wallafa bidiyon inda jama'a da dama suke caccakar Okpebholo da ma APC baki daya.

"Za mu samar muku da rashin tsaro."

- Monday Okpebholo

Oshiomhole ya ci gyaran dan takarar gwamna

An cikin faifan bidiyon, an gano Sanata Adams Oshiomhole da ke wakiltar Edo ta Arewa yana yi masa gyara.

Daga bisani, Okpebholo ya gyara maganarsa, sai dai duk da gyaran da ya yi yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu inda wasu ke caccakar shi.

Wasu da dama sun bayyana cewa daman babu abin da APC ta kware sai kawo rashin tsaro kamar yadda ya fada.

Kara karanta wannan

Gwamma ya kafa kwamiti, zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000

Sai dai wasu sun bayyana cewa kuskure ne kowa zai iya yi musamman idan yana shiga harkokin jama'a.

Obaseki ya fadi silar fadansa da Oshiomhole

Kun ji cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana ainihin abin da hada shi faɗa da Sanata Adams Oshiomhole.

Obaseki ya ce rikicin ya fara ne tun bayan mutuwar jigon PDP, Cif Tony Anenih wanda ya dauki nauyin jana'izarsa a gwamnatance.

Sai dai ya ce Oshiomhole ya kalubalanci hakan inda ya ce bai kamata ba saboda bai rike da wani mukami a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.