2027: Tafiyar Shekarau na Kara Ƙarfi da Namadi Sambo da Ministan Buhari Suka Goyi Baya

2027: Tafiyar Shekarau na Kara Ƙarfi da Namadi Sambo da Ministan Buhari Suka Goyi Baya

  • Kungiyar League of Northern Democrats (NLD) ta samu karin karfi da goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo
  • Kungiyar ta aka kafa domin kawo sauyi a Najeriya musamman a Arewacin Najeriya ta na cigaba da samun karɓuwa
  • Bayan Namadi Sambo, tsohon hafsan sojoji, Laftanar janar Abdulrahman Dambazau shi ma ya nuna goyon bayansa ga kungiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya goyi bayan gamayyar League of Northern Democrats (LND.

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau shi ke jagorantar ƙungiyar domin kawo sauyi a Najeriya.

Namadi Sambo da Ministan Buhari sun shiga tafiyar Shekarau
Namadi Sambo ya yaba da tafiyar kungiyar Mallam Ibrahim Shekarau. Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau, Namadi Sambo.
Asali: Facebook

LND: Shekarau ya samu karin karfi

Namadi Sambo ya fadi haka ne bayan karbar bakwancin kungiyar karkashin jagorancin Shekaru a Kaduna, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Babban hadimin Shugaba Tinubu ya ajiye aikinsa, ya jero dalilai masu ƙarfi

The Nation ta ruwaito cewa Sambo ya bayyana cewa abin takaici ne yadda rashin tsaro ya kawo tsaiko a harkokin noma da ilimi a Arewacin Najeriya.

"Babu dadi yadda rashin ya lalata harkokin noma da ilimi da kuma ɓangaren lafiyar yara da mata."
"Wannan matsala ta sake kara talauci a tsakanin al'umma da rashin daidaito a Arewa dama kasa baki daya."

- Namadi Sambo

Dambazau ya goyi bayan tafiyar Shekarau

A bangarensa, tsohon hafsan sojoji, Laftanar janar Abdulrahman Dambazau ya ce yadda komai ya lalace a Arewa yana bukatar matakin gaggawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, tsohon Ministan ya yabawa kungiyar a kokarin kawo sauyi a matsalolin yankin.

Ya yi alkawarin shiga lamuran ƙungiyar domin ba da ta shi gudunmawa wurin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Bayan tura sojoji Sakkwato, 'yan Arewa sun fara shinshino karshen rashin tsaro

Dr. Umar Ardo shi ya kafa kungiyar inda aka ba Mallam Ibrahim Shekarau mukaddashin shugabanta.

2027: Shekarau na jagorantar tafiya mai karfi

Kun ji cewa da alamu an sake taso Shugaba Bola Tinubu a gaba a zaben 2027 inda wasu jiga-jigai a Arewacin kasar nan suka fara shiri.

Kungiyar League of Northern Democrats da Ibrahim Shekarau yake jagoranta suna neman fadada shirinsu zuwa Kudu.

Kungiyar ta bayyana cewa ganin yadda Tinubu ya gina siyasarsa, zai yi wahala a iya kawar da shi daga mulki cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.