Kwankwaso Ya Bugi Kirji kan Zaben 2027, Ya Fadi Abin da Zai Faru
- Rabiu Musa Kwankwaso jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa ya yi magana kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ake tunkara
- Kwankwaso ya bayyana cewa zai samu nasara a zaɓen na 2027 kuma jam'iyyar NNPP a shirye take ta karɓi ragamar jagorancin ƙasar nan
- Madugun na Kwankwasiyya ya shawarci ƴan Najeriya da ka da su yarda a yaudare su da taliya ko kuɗi a lokacin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabi'u Kwankwaso, ya ce zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, wanda ya zo na huɗu a zaben, ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar a birnin Katsina.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ƙaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP, da ke kan titin IBB, a birnin Katsina.
Kwankwaso ya ke Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya ga iyalan Yar’adua bisa rasuwar Hajiya Dada, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.
Me Kwankwaso ya ce kan zaɓen 2027?
A cewarsa, jam’iyyar a shirye take ta karɓi ragamar shugabancin ƙasa, jihohi da sauran muƙamai a fadin ƙasar nan zuwa 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar na kan hanyar samun nasara a zaɓen 2027 mai zuwa.
"Ina so na tunatar da ku cewa, jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, domin muna cikin jam’iyyar, tunda sun fita daga kan layi, mun yanke shawarar taka musu birki."
Rabiu Musa Kwankwaso
Ya yi kira ga ƴan Najeriya musamman mata da matasa da kada su bari a yaudare su da taliya ko kuɗi a lokacin zaɓe mai zuwa.
Kwankwaso ba zai iya cin zaɓe ba
Wani ɗan jam'iyyar NNPP a jihar Kano mai suna Ibrahim Muhammad ya gayawa Legit Hausa cewa Kwankwaso ba zai iya cin zaɓe shi kaɗai ba.
Ya bayyana cewa idan dai har ba haɗaka aka yi tsakanin ƴan adawa ba, jagoran na Kwankwasiyya ba zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027 ba.
"Gaskiya idan dai har ba haɗaka aka yi tsakanin shi da su Atiku ba, ba na tunanin zai iya cin zaɓen shugaban ƙasa. Har yanzu jam'iyyar mu ba ta yi kafuwar da za ta iya cin zaɓen shugaban ƙasa ba."
- Ibrahim Muhammad
Tsohon jigo a APC ya ba Kwankwaso shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa a yankin Arewa ta yamma, Lukman Salihu ya yi kira na musamman ga yan jam'iyyun adawa.
Lukman Salihu ya bukaci Atiku Abubakar, Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi su hada kai domin kawo karshen mulkin APC a Najeriya.
Asali: Legit.ng