"Zai Ɗan Yi Ƙiba": Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Hadimin Tinubu Ya Ajiye Aikinsa
- Sanata Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa bayan murabus din Ajuri Ngelale a yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024
- Sanatan ya ce a yanzu Ajuri zai samu ya huta ya kashe wayarsa da kuma bacci da cin abinci sosai har ma ya yi kiba
- Wannan na zuwa ne bayan tsohon hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa ya ajiye aikinsa saboda dalilai na iyalansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani ya yi magana bayan murabus din hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya ya ce a yanzu ne Ngelale zai dan samu ya yi kiba saboda hutu.
Ajuri Ngelale: Shehu Sani ya yi martani
Shehu Sani ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya ce Ngelale zai kwanta ya yi bacci ya huta har ma ya dan samu ya yi kiba.
Ya ce tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu yanzu zai iya kashe wayarsa ya huta sosai.
"Ajuri yanzu zai huta sosai, ya yi bacci sosai, ya ci abinci da kyau."
"Zai kashe wayarsa saboda hutu har ma ya dan samu ya yi kiba kadan."
Musabbabin ajiye aiki da Ajuri Ngelale ya yi
Martanin tsohon sanatan na zuwa ne bayan Ajuri Ngelale ya sanar da murabus dinsa a yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.
Ajuri ya tabbatar da a haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tsohon hadimin ya ce ya ajiye aikin ne saboda kula da matsalar rashin lafiya da ta shafi iyalansa.
Ya yi godiya da damar da ya samu inda ya ce idan kaddara da lokaci sun dawo da shi zai cigaba da aiki ga Gwamnatin Tarayya.
Tinubu ya kare matakin karin farashin mai
Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan karin farashin mai da aka samu a fadin Najeriya.
Tinubu ya ce daukar wasu matakai masu tsauri sun zama dole domin samun damar kawo cigaba a kasar.
Asali: Legit.ng