Babban Hadimin Shugaba Tinubu Ya Ajiye Aikinsa, Ya Jero Dalilai Masu Ƙarfi

Babban Hadimin Shugaba Tinubu Ya Ajiye Aikinsa, Ya Jero Dalilai Masu Ƙarfi

  • Yayin da Shugaba Bola Tinubu ke kasar China, babban hadiminsa a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya yi murabus
  • Ngelale ya tabbatar da mika takardar murabus din ne ga shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila
  • Tsohon hadimin shugaban ya bayyana cewa ya ajiye aikin ne domin kula da lafiyar iyalansa da sauran matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hadimin Shugaba Bola Tinubu a ɓangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya yi murabus daga mukaminsa.

Ngelale ya yi murabus din ne saboda ba da hankali wurin kula da lafiyar iyalansa kamar yadda ya tabbatar.

Hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa a gwamnatin APC
Babban Hadimin Shugaba Tinubu a Bangaren Sadarwa, Ajuri Ngelale Ya Ajiye Aikinsa. Hoto: Ajuri Ngelale.
Asali: Twitter

Hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa a gwamnatin APC

Tsohon hadimin ya bayyana haka a shafinsa na Facebook da safiyar yau Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

An soki Barau Jibrin kan karbar mutane zuwa APC alhali ana kukan kuncin rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ngelale ya mika takardar murabus din na shi ne ga shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila a jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024.

"Na dauki wannan mataki maras dadi ne bayan tattaunawa da yan uwana kan matsalolin rashin lafiya na tsawon kwanaki da ya yi kamari."
"Ina tsammanin dawowa bakin aiki duk lokacin da ƙaddara ta tabbatar da hakan domin cigaba da ba da gudunmawa ga kasa."

- Ajuri Ngelale

Ngelale bai bayyana lokacin dawowa aiki ba

Sai dai Ngelale bai bayyana lokacin dawowarsa bakin aiki ba saboda a cikin sanarwar ya tabbatar da cewa ba rana.

Ngelale daga bisani ya bukaci sirri game da rayuwarsa da kuma na iyalansa a daidai wannan lokaci bayan ajiye aikinsa.

Hakan na zuwa ne yayin da maigidansa, Tinubu ke kasar China inda ya bayyana nasarorin da aka samu yayin ziyarar.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Tinubu ya magantu kan karin farashin mai

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci yan Najeriya mazauna China da su tabbatar da sun wakilci kasarsu a ketare.

Tinubu ya fadi irin nasarorin da ya samu yayin ziyarar kwanaki da ya yi kasar China inda ya sake rokon yan Najeriya.

Shugaban ya bayyana amfanin karin kudin mai inda ya ce ba tare da samun kudin shiga ba, babu damar yin ayyukan alheri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.