"Ku Taimake Mu": Gwamna a Arewa Ya Sallami Shugabannin Kananan Hukumomi 17

"Ku Taimake Mu": Gwamna a Arewa Ya Sallami Shugabannin Kananan Hukumomi 17

  • Gwamnatin jihar Plateau ta kori dukan shugabannin kananan hukumomi 17 a jihar bayan wa'adinsu ya kare
  • Gwamna Caleb Mutfwang shi ya ba da wannan umarni inda ya godewa tsofaffin shugabannin kananan hukumomin
  • Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Gyang Bere ya fitar a daren jiya Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya sallami dukan shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Gwamnan ya kori shugabannin rikon ne guda 17 da aka naɗa su a watan Yunin 2023 da zimmar yin wa'adin watanni shida.

Gwamna ya fatattaki shugabannin kananan hukumomi 17 a jiharsa
Gwamna Caleb Mutfwang ya kori shugabannin kananan hukumomi 17 a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Plateau: Yaushe za a yi zaɓen kananan hukumomi?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darakatn yada labaransa, Gyang Bere fitar a jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an nada su ne tun a watan Yunin 2023 amma an yi ta kara wa'adin har zuwa jiya Juma'a kafin korarsu.

Bere ya umarci daraktocin gudanarwa na ƙananan hukumomin 17 su karbi ragamar shugabancin har zuwa 9 ga watan Oktoban 2023 da za a yi zabe.

"Gwamna Mutfwang ya godewa shugabannin kananan hukumomin masu barin gado saboda ayyukan raya kasa da suka yi."
"Ya kuma bukace su da su ci gaba da ba da gudunmawa wurin samar da zaman lafiya a Plateau da jam'iyyar PDP."

- Gyang Bere

Gwamna Mutfwang ya roki tsofaffin ciyamomi

Gwamna Mutfwang daga bisani ya roki tsofaffin ciyamomin su hada kai da yan takara domin tabbatar da nasarar PDP a zabukan.

Ya tabbatar da himmatuwar gwamnatinsa wurin samar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al'umma, cewar rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

Gwamna Mutfwang ya kori jami'an gwamnati

Kun ji cewa Mai grma Gwamnan jihar Plateau ya ɗauki matakin dakatar da wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa.

Caleb Mutfwang ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu manyan jami'an gwamnati mutum biyu daga kan muƙamansu.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ƙara da cewa dakatarwar ta fara aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.